Ina nan a APC – Hon. Bello Bakyasuwa

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Tsohon sakataren yaɗa labarai na ɓangaren jam’iyyar APC ta Sanata Kabiru Marafa a Jihar Zamfara Muhammad Bello Soja Bakyasuwa, ya jaddada cewar yana nan a jam’iyyar APC a ƙarƙashin jagorancin ƙaramin ministan tsaro Hon. Dr. Muhammad Bello Matawalle MON da Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar.

Bello Bakyasuwa tsohon darakta a harkokin tsaro na gwamnatin Jihar Zamfara, kuma tsohon kwamandan hukumar yaƙi da ‘yan ta’adda ta Zamfara ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Gusau yau Juma’a.

Bakyasuwa ya ƙara da cewa zai cigaba da kasancewa memba a jam’iyyar APC, yana mai ƙarawa da cewa ba ya tare da Sanata Kabiru Garba Marafa wanda ya bar jam’iyyar kwanan nan.

“Ba na goyon bayan Sanata Marafa wanda aka sanar kwanan nan cewa ya bar APC kuma zan yi duk abin da zan iya don inganta ƙarfin jam’iyyar.

“Ina so in sanar da mutanen Zamfara cewa ban fice daga jam’iyyar APC ba kuma zan ci gaba da aiki don ci gaban jam’iyyar a jihar Zamfara ƙarƙashin jagorancin mai girma Bello Matawalle da Sanata Abdul’aziz Yari,” in ji shi.

Bakyasuwa ya ƙara da cewa zai yi aiki don ganin Shugaba, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya yi nasara a Zamfara a babban zaɓen 2027.

Ya yi kira ga magoya bayansa da su ci gaba da kasancewa masu haɗin kai da bin doka don ci gaban APC da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027 a jihar.

By ukarofi