‘Yan sanda sun musanta janye jami’an tsaron Atiku, Wike da wasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rundunar ƴan sanda ta musanta rahoton da ake yaɗawa akan janye jami’an tsaron wasu manyan mutane a Nijeriya.

A wani saƙo da ta wallafa ta kafar X a yau Juma’a, rundunar, ta baki kakakinta Benjamin Hundeyin, ta ce rahoton, wanda aka yi zargin CSP Abdullahi Sulaiman da aka bayyana daga sashen gudanarwa ne yake ya sanya wa hannu, ba gaskiya ba ne kuma abu ne da ake yaɗawa da nufin ruɗar da al’umma.

Waɗanda aka lissafo sun haɗa da : Atiku Abubakar, Namadi Sambo, Nyesom Wike, Aisha Buhari, Justice Kudirat Olatokunbo Kekere-Ekun, HRM Ogiame Atuwatse III, Ngozi Iweala, Senator Ahmed Lawal, Senator Tanko Almakura, Dr. Ramatu Tijjani, Hon. Yusuf Gagdi, Hon. Ibrahim Massari da daia sauran su.

Rundunar ta ƙara da cewa, ba ta da masaniya akan wannan takardar don haka abu ne na ƙarya da nufin rikitar da jama’a.

Tuni Hundeyin ya ce sun fara aiwatar da umarnin Shugaba Bola Tinubu na janye jami’an ƴan sanda daga tsaron manyan mutane.

Kazalika, ya bayyana cewa aikin aiwatar da umarnin abu ne da ake yi mataki-mataki tare da amfani da ƙwarewa domin kauye wa kurakurai.

By Babaji