
Rahotanni daga Jihar Kebbi sun tabbatar da mutuwar jami’an hukumar shige-da-fice su guda uku sakamakon wani hari da mayaƙan Lakurawa suka kai kan gidajen kwanansu da ke yankin shingen bincike.
A jiya Alhamis da dare aka kai harin a ƙauyen Bakin ruwa na Ƙaramar Hukumar Bagudo da ke da iyaka da Jamhuriyar Benin.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin cikin gida na jihar, Haliru Aliyu Wasagu, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ƴan bindigar sun cinna wa gidajen ma’aikatan wuta ne cikin daren, sannan bayan sun fito daga gidan kuma suka harbe su har aka kashe 3 tare da jikkata ɗaya.
Ya kuma ce, an tura jam’ian tsaro yankin domin su maido da zaman lafiya, tare da farauto waɗanda suka aikata ta’asar.
Aliyu Wasagu ya ƙara da cewa zuwa yanzu ba a san dalilin da ya sa suka kai wa jam’ian tsaron hari ba, sai dai ya ce sau tari mayaƙan Lakurawa kan kai wa jami’an tsaro hari, amma ana gudanar da bincike.
A watan Yuni sun kashe ƴan sanda uku, haka ma a kwanakin baya kuma sun hallaka wasu jami’an kwastam a duk a jihar.

