Zan yi murabus matuƙar Tinubu ya faɗi a zaɓen 2027, inji Gwamna Okpebholo na Edo

Spread the love

Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya ce a shirye yake ya yi murabus daga muƙaminsa matuƙar Shugaba Bola Tinubu ya gaza lashe jiharsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Okpebholo ya lura cewa jam’iyyar APC a yanzu ta mamaye siyasar jihar Edo gaba ɗaya, kuma ba ta fuskantar wata adawa gabanin babban zaɓen mai zuwa, wanda ake sa rana gudanarwa nan da watanni 15.

Da yake magana a wata hira da gidan talabijin na AIT, Okpebholo ya ce Tinubu na da goyon baya mafi rinjaye a Edo don haka yake fatan shugaban ƙasar ya lashe zaɓen da ƙuri’a mai yawa.

Ya bayyana cewa, karɓuwar gwamnatinsa da ke ƙaruwa yanzu na da alaƙa kai-tsaye da tasirin shugaban ƙasa a mulkinsa.

“Asiwaju ma ya fi ni farin jini a nan yanzu saboda mutanen Edo sun riga sun fahimci cewa abubuwan da nake yi sakamakon tasirin Asiwaju ne,” inji gwamnan.

“Za ku ga irin sakamakon da zai fito daga nan saboda babu wasu masu adawa a Edo”, kamar yadda ya ƙara a zancen nasa.

By Babaji