
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa kuma ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, wato Bello El-Rufai, ya ƙalubalanci tsarin shari’a a Nijeriya inda ya yi kira da ƙara ƙaimi wajen tabbatar da kiyaye gaskiya da adalci a fannin.
Bello ya bayyana haka ne yayin zaman majalisar inda ya soki hukuncin ɗaurin rai-da-rai ga Nnamdi Kanu yayin da kuma aka yanke hukuncin shekara 20 ga jagoran ƴan ta’addan Ansaru mai suna Husseini Ismail da ya jagoranci ayyukan ta’addanci daban-daban.
Kalaman ɗan majalisar sun haddasa muhawara mai zafi a faɗin ƙasa bayan da ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda ake aiwatar da shari’a a Nijeriya cikin rashin daidaito.
A cewarsa, abin takaici ne a yanke wa Mazi Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai, yayin da wasu ‘yan ta’adda na Boko Haram da aka tabbatar da laifin kashe mutane, su ke samu da shekara 20 kacal a gidan yari.
Bello El-Rufai ya tambayi abin da jama’a ke ta ɓoyewa a ransu na tsawon shekaru a ƙasar, wato “Me ya sa shari’a ke tafiya da bambanci a Nijeriya?”
“Adalci ya zama na kowa, ba na wasu ƙabilu ko na wasu matsayi ba.” inji ɗan majalisar.
