Legas: Shugaban ’Yan Arewa a Epe ya buƙaci ƙarin haɗin kai tsakanin mambobi

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

Shugaban ƙungiyar ’Yan Arewa na ƙaramar Hukumar Epe a Jihar Legas, Alhaji Ummaru Gwamna Epe, ya shawarci shugabanni da mambobin kungiyar a faɗin jihar da su ƙara haɗa kai da zaman tafiya a tsari ɗaya domin ƙarfafa martabar al’ummar Arewa a Legas.

Alhaji Gwamna Epe ya yi wannan kira ne a garin Epe yayin wani taron tattaunawa da ya gudanar tare da wasu jiga-jigan ƙungiyar, wanda yake kanana shugabanci ke gudanarwa a ƙarshen kowane mako domin nazari kan matsaloli da kuma ɗaukar matakan magance su.

Ya bayyana cewa, hadin kai da kyakkyawar fahimta ita ce hanya mafi inganci ta bunƙasa ƙungiyar da ɗaukaka martabar al’ummar Arewa a Legas da kewaye.

Ya ƙara da cewa, ya lura da wasu mambobi masu ƙoƙarin kawo rabuwar kawuna, inda ya jaddada cewa irin waɗannan ɗabi’u suna jawo tarnaki ga ci gaban kowa.

A cewarsa, “Abin da ake buƙata shi ne mu yi magana da murya ɗaya. Idan muka tsaya tsayin daka mu hada kai, babu abinda zai kasa yiwuwa wajen kare muradinmu da kare mutuncin Arewa a Legas.”

Alhaji Gwamna ya yabawa shugaban ƙungiyar Arewa Kwaminiti na Jihar Legas, Alhaji Sa’adu Yusuf Dandare Gulma, bisa himma da jajircewarsa wurin sake gina tsarin ƙungiyar da tabbatar da zaman lafiya tsakanin mambobi. Ya ce tun zuwansa jagoranci, an samu kyakkyawan sauyi duk da ƙalubalen da aka fuskanta a baya.

Ya kuma gargaɗi ‘yan tsirarun da ke ƙoƙarin tayar da husuma da rikita kawunan al’umma, yana mai cewa maimakon haka ya dace su taimaka wajen samar da cigaba da bunƙasa ƙungiya.

Daga ƙarshe, ya yi addu’ar samun zaman lafiya da cigaba ga Nijeriya, tare da kira ga al’ummar Arewa mazauna jihar Legas da su ci gaba da zaman lafiya da sauran ƙabilu domin ɗorewar haɗin kai da zaman lafiya.

By ukarofi