Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Alƙalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, Mai Shari’a Joyce Abdulmalik, ta kori shari’ar da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta shigar kan wasu manyan jami’an Hukumar Zaɓen ƙananan Hukumomi ta Jihar Kano (KANSIEC).
Jami’an da abin ya shafa sun haɗa da Shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Lawal Malumfashi; Sakataren Hukumar, Anas Muhammed Mustapha; da Daraktan Kuɗi na Hukumar, Ado Garba.
An tsara shari’ar mai lamba FHC/ABJ/210/2025 domin gurfanar da su a gaban kotu ranar Litinin, amma zaman bai ci gaba ba saboda waɗanda ake tuhuma ba su bayyana a kotu ba.
Ana tuhumar su da laifuka guda 10 da suka shafi zargin badaƙalar Naira biliyan 1.02 a lokacin zaɓukan ƙananan hukumomi na 2024.
A zaman da ya gabata, Lauyan ICPC, Enosa Omoghibo, Mataimakin Darakta a Sashen Shari’a na hukumar, ya shaida wa kotu cewa: “An tsara yau domin gurfanar da su, amma waɗanda ake tuhuma ba su zo kotu ba.”
Sai dai Lauyan kariya, M.A. Magaji, SAN, ya ce ba a sanar da waɗanda ake tuhuma takardun tuhuma da sauran takardun kotu ba. Ya jaddada cewa bayar da takardar sammaci yadda ya dace abu ne muhimmi wajen tabbatar da hurumin kotu.
Mai Shari’a Abdulmalik ta dage zaman zuwa Litinin, 24 ga Nuwamba, domin ba da damar tabbatar da isar da takardu yadda ya kamata da kuma tabbatar da zuwan dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.
A ranar Litinin da aka sake kiran shari’ar domin gurfanar da su, waɗanda ake tuhuma ba su bayyana ba, lamarin da ya sa alƙaliyar ta kori shari’ar.
