An yi garkuwa da basarake a Kwara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da wani sarki mai suna Oba Kamilu Salami, wanda shi ne Ojibara na Masarautar Bayagan da ke Ƙaramar Hukumar Ifelodun a Jihar Kwara.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya ƙara jefa al’umma cikin firgici duba da yadda al’amarin tsaro ke taɓarɓarewa a ƙauyukan da ke sassan jihar.

An gano cewa, an sace sarkin ne a safiyar jiya Asabar a gonarsa, saidai babu cikakken bayani akan al’amarin yayin haɗa wannan rahoton.

Mazauna yankin sun ce harin ya faru ne kwatsam wanda ya je sun cikin tsoro da rikicewa.

Hukumomin tsaro a jihar ba su fitar da saƙon na musamman akan al’amarin ba zuwa yanzu.

By Babaji