
Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Jihar Kano, ta ƙaddamar da karatun musabaƙa na yara da matasa a Cibiyar Musulunci dake yankin.
A sanarwar da Jami’ar Yada Labarai ta karamar hukumar, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta raba wa manema labarai, an ƙaddamar da kwamitin gasar ne domin zaburar da al’umma koyo da karatun musabakar karkashin Gwamnatin Abba Kabir Yusuf na jihar, don kwadaituwa da karanta Al-Kur’ani mai girma tare da aiki da shi a kodayaushe.
Shugaban Kwamitin Musabakar na yankin, Malam Ibrahim Muhammad, ya bayyana Bichi tana cikin kananan hukumomin da aka fara gudanar da wannan gasa ta musabakar Kur’ani da ta kunshi rukunai biyar; daga kan masu izufi 2 da 10 da 20 da 30 da kuma ‘yan izufi 60.
Ya ce, kowane rukuni za a ɗauki waɗanda suka zo na ɗaya zuwa na uku domin a ba su kyaututtuka.
Ya cigaba da cewa, Injiniya Abba Kabir Yusuf aikinsa ne bayar da kyakkyawar kulawa a wannan bangare na hidimtawa littafin Allah mai girma.
Kazalika, ya yi karin haske, wannan musabaka ce da aka yi wa lakani da Musabaka Abba Gida-Gida 2025 da za ta game lungu da sako ko’ina, kasancewar gasar ba a iya matakin kananan hukumomi kadai ta tsaya ba.
“Kowace karamar hukuma za a yi wannan gasa, daga nan kuma za a yi ta shiyya-shiyya sannan kuma a ti a matakin jiha. Muna gode wa mai girma Gwamna da wannan tsari tare da kaunar makarantun islamiyya da na allo da yake yi.”
Malam Ibrahim, ya ja hankalin iyaye kulawa da tura yara makaranta akan lokaci tare da kaucewa aikensu ko saka su wani aiki a lokutan karatu, musamman bayan asuba zuwa hantsi, domin kwalliya ta biya kudin sabulu yadda yakamata.
Shugaban Makarantar Riyadul Kur’an Islamiyya Bichi, Malam Muhammad S Muhammad, ya ce, assasa musabaka ta Al-Kur’ani abu ne mai kyau da zai zaburar da yara kokarin karanta Kur’ani wajen fahimtar da su addini yadda yakamata. Don haka ya ja hankalin malamai a kan su kula da inganta wannan aikin alheri da gwamnatin Kano ta assasa.
“Su kansu malaman makarantu ya kamata su zage damtse kuma su dinga dogaro da kansu a daina kashe wa yara gwiwa wajen yunkurin aro wasu dalibai daga wanu wuri, lallai ne mu rika rainon namu har su girma su tsare mutumcin karamar hukumarsu da jiharsu har ya zuwa kasa baki daya.”
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata, wanda ya samu wakilcin kansilan WESH, ya yi addu’a da fatan samun nasara a dukkan matakan gasar.





