ADC ta gama shirin kayar da Tinubu a zaɓen 2027 – Hon. Ungoggo

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Shugaban Jam’iyyar ADC na Jihar Kano, Hon. Musa Shuaibu Ungoggo, ya bayyana cewa jam’iyyarsu ta gama shiri tsaf domin fafatawa da karbar mulki daga jam’iyyar APC a zaɓen 2027, kasancewar gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta nuna gazawa a fannoni daban-daban na rayuwa.

Hon. Ungoggo ya yi wannan bayani ne a wajen taron shugabannin jam’iyyar ADC daga ƙananan hukumomi 44 na Kano, wanda aka gudanar a gidan tunawa da marigayi Malam Aminu Kano (Mambayya House) a makon da ya gabata.

Ya ce taɓarɓarewar tsaro a ƙasar nan ya kai wani mawuyacin matsayi, inda ya bayyana cewa “a yau akwai garuruwa sama da 180 da suka zama kufai—ba kowa a cikinsu—saboda ayyukan ‘yan bindiga irin su Bello Turji, wanda saboda tsananin rikicewar tsaro ya zama kamar wani jigo a arewa.”

Ungoggo ya ci gaba da cewa bisa ga wannan gazawa ta gwamnati a fannoni kamar tsaro, ilimi, lafiya, da tattalin arziki, al’umma ba su da wani zabi a 2027 face ADC domin APC da PDP sun gaza a lokuta daban-daban.

A ƙarshe, shugaban ADC na Kano ya jaddada cewa jam’iyyarsu za ta yi aiki tukuru domin dawo da Nijeriya kan turbar zaman lafiya, adalci, da ci gaba. Ya tunatar da tarihin siyasa a Kano da Nijeriya tun 1979, inda ya ce lokuta da dama jam’iyyun da ake tsammani za su yi nasara suna faduwa saboda al’amura na ikon Allah. Ya kawo misalai da zaben 1983 tsakanin Rimi da Sabo Bakin Zuwo, da 2003 tsakanin Shekarau da Kwankwaso, da 2011, 2019 da 2023 inda Abba Kabir Yusuf ya kada gwamnatin da ke hannunta.

Ya ce duk yawan shugabanni ko ‘yan majalisu da ke komawa APC “kamar ana cinikin shanu, kowa da farashinsa,” ba zai hana ADC nasara ba, domin jama’a sun gaji kuma suna neman sauyi mai ma’ana.

By ukarofi