Daga AISHA ASAS
Daga 2020 zuwa 2025, nahiyar Afirka ta sake shiga wani sabon zamani na rikice-rikicen siyasa, inda aƙalla juyin mulki 10 suka faru, musamman a yankin Yammacin Afirka da Sahel.
Sabon juyin mulki a Guinea-Bissau a ranar 26 ga Nuwamba, 2025, ya cika jerin juyin mulki 10 da suka faru tun 2020, wanda ya haifar da matuƙar damuwa daga ECOWAS, Tarayyar Afirka da sauran ƙasashen duniya.
Da wannan ne Blueprint Manhaja ta yi duba kan jerin juyin mulkin da suka faru tun 2020 kawo wa yanzu, wanɗada za mu bayyana maku a wannan mako:
1. Mali – 2020 da 2021:
Sojoji ƙarƙashin jagorancin Colonel Assimi Goita sun kifar da gwamnatin Keita a 2020, sannan suka sake karɓar mulki daga gwamnatin riƙon kwarya a 2021.
Goita ya tsawaita wa’adinsa da shekaru biyar a 2025.
2. Chadi – 2021:
Bayan rasuwar Idriss Déby, sojoji suka kafa Mahamat Déby a matsayin shugaban riƙon kwarya, suka warware kundin tsarin mulki, sannan suka tabbatar da shi a zaɓen 2024 mai cike da cece-kuce.
3. Guinea – 2021:
Lt-Col Doumbouya ya hamɓarar da Alpha Condé.
A 2025 ya sanar da tsayawa takarar shugabanci yayin da ake shirin zaɓen dawo da mulki ga farar hula a ƙarshen shekara.
4. Sudan – 2021:
Burhan ya kifar da gwamnatin haɗaka bayan tashin hankali tsakanin manyan jami’an soji da farar hula.
Daga 2023 zuwa yau, Sudan na cikin mummunan yaƙi tsakanin sojojin Sudan da RSF, wanda ya hallaka dubban mutane.
5. Burkina Faso – 2022 ɗ2:
A Janairu 2022 Damiba ya hamɓarar da Kabore.
A Satumba 2022 Traore ya hamɓarar da Damiba.
A 2024, aka ba Traore ƙarin shekaru 5 saboda tashin hankali na ’yan ta’adda.
6. Nijar – 2023:
Gwamnatin Bazoum ta faɗi bayan rundunar tsaron fadar shugaban ƙasa ta yi juyin mulki.
A 2025, rundunar sojin ta tsawaita mulkinsu da akalla shekaru biyar.
7. Gabon – 2023:
An hamɓarar da Ali Bongo bayan shekaru 55 na mulkin iyalan Bongo.
General Nguema ya zama shugaban riƙon ƙwarya sannan ya zama shugaban ƙasa da ƙuri’a 94% a 2025.
8. Madagascar – 2025:
Daga zanga-zangar Gen Z, sojoji suka hamɓarar da Rajoelina, suka naɗa Colonel Randrianirina mai alƙawarin zaɓe cikin shekara 1–2.
9. Guinea-Bissau – 2025:
A ranar 26 ga Nuwamba, sojoji suka hamɓarar da Embalo, suka soke zaɓe, suka ɗauke ikon gwamnati gaba ɗaya.
ECOWAS ta dakatar da ƙasar.
10. Burkina Faso (jinjina ta biyu) – biyo bayan tasirin Sahel
Ana ƙara kallon Burkina Faso a matsayin misalin yadda juyin mulki ke bazuwa a Sahel saboda tsaro da matsin tattalin arziki.
Jerin juyin mulkin da ke faruwa a Afirka ya sake tunasar da irin raunin tsarin siyasa a nahiyar. Rashin tsaro, talauci, matsin tattalin arziki, zaɓen da ake zargin an yi maguɗi da kuma gazawar hukumomi na daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da juyin mulki.
