Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ƙungiyar Muryar Matasa mai suna ‘Matasa Initiative For Employment Development And Inclusion, ta shirya biki na al’adu da kuma wasanni daban-daban mai taken “Matasa, kasuwanci da Al’adu’ a filin wasa na Muhammad Dikko, a garin Katsina.
Wasannin da aka shirya ya gudana cikin tsari mai kyau da nishaɗantarwa, inda aka mayar da hankali kan bunƙasa kasuwancin matasa a fannoni uku: Kasuwanci, Al’adu da Wasanni.
Shugabar taron Saratu Hamidu Samaila, ta ce sun shirya taron ne domin nuna ma jama’a cewa su ma mutāne masu buƙata ta musamman suna bada gudunmuwa da goyan baya wajen haɓaka tattalin arziki, zaman lafiya da kuma samun haɗuwar kan jama’a a jihar da ƙasa baki ɗaya.
Ta kuma ce wannan taro shi ne karo na farko da suka shirya a Katsina wanda za su ci gaba da shirya wa a duk shekara domin ƙara ƙarfafawa matasa ƙwarin gwiwa.
Shirin ya kasance wani dandali na ilmantarwa da ƙirƙire-ƙirƙire, inda matasa suka fafata a fannoni da suka haɗa da kacici-kacici da kuma bayar da amsar tambayoyin kai-tsaye, da suka shafi al’amurran yau da kullum, wasa ƙwaƙwalwa, rige-rigen cin abinci, da wasan tsintar ƙwallaye ga masu lalurar idanu, domin ƙarfafa halartar masu buƙata ta musamman.
A ɓangaren kasuwanci, shirin ya samar da baje koli domin matasa masu ƙananan sana’o’i su gabatar da kayayyakin da suka ƙirƙira.
Shirin dai, ya ja hankalin ‘yan kasuwa da masu saka jari da suka samu halarta, domin duba sabbin hanyoyin bunƙasa tattalin arziki.
A ɓangaren al’adu kuwa, an nishaɗantu ne da rera wakoki daga manyan mawaƙa da mawaka masu tasowa, tare da waƙar baka (Poetry) daga Aisha Mukhtar Muttaka, da kuma tseren kekuna na masu lalurar ƙafa da wasu wasanni masu jan hankali.
Taron ya samu halartar manyan mutane, jami’an gwamnati, ƙungiyoyin farar hula, ’yan kasuwa da jama’a masu buƙata ta musamman, waɗanda suka yaba da yadda shirin ya mayar da hankali kan inganta ƙwarewa, gina tunani da ƙarfafa matasa su shiga sahun ci gaban tattalin arziki da al’adu.
Taron wanda ya ƙayatar kuma tattaro matasa da masu ruwa da tsaki a harkokin ci gaban al’umma, da aka shirya a filin wasa na Muhammad Dikko a Katsina.
