
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Majalisar Dattawa ta amince da buƙatar Shugaba Bola Tinubu ta tura jami’an sojoji zuwa Jamhuriyar Benin domin taimaka wa ƙoƙarin ƙasar na dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Hakan na zuwa ne ƙasa da mako guda da aka yi yunƙurin kifar da gwamnatin dimukraɗiyyar ƙasar.
Da fari, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya sanar da batun yayin zamansu na yau Talata, wanda daga bisani suka cimma matsayar amince wa buƙatar bayan nazari a kai.
Lamarin da ya nuna goyon bayansu ga yunƙurin tallafin na lamuran tsaro a shiyyar.
Akpabio ya bayyana matakin a matsayin abin da ya dace a yanzu, musamman duba da halin taɓarɓarewar tsaro da ke addabar sassan baki ɗaya shiyyar.
Ya ce, wajibi ne Nijeriya ta ba ƙawayenta na ECOWAS tallafi domin cigaba da ƙarfafa alaƙar da ke tsananinsu.
A ranar Lahadi, aka yi yunƙurin kifar da gwamnatin Jamhuriyar Benin a lokacin da wasu tsirarun sojoji suka sanar da tsige Shugaba Patrice Talon na ƙasar.
