
Ƙungiyar Ci-gaban Tattalin Arziƙin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS), ta ayyana dokar ta-baci a faɗin yankin yammacin Afirka sakamakon ƙalubalen tsaro da juyin mulki da ke ƙaruwa a wasu ƙasashen mambobinta.
Wannan mataki na zuwa ne a matsayin martani ga hauhawar barazanar tsaro, musamman juyin mulki a wasu ƙasashe, da kuma yunƙurin dawo da tsarin dimokuraɗiyya da zaman lafiya a yankin.
A cewar shugabannin ECOWAS, wannan dokar ta-baci za ta bai wa ƙungiyar damar ɗaukar matakan gaggawa don kare dimokuraɗiyya, samar da zaman lafiya da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Za a ci gaba da bibiyar wannan mataki don ganin yadda zai shafi ƙasashen yankin.
A watan da ya gabata ne wata tawagar sojoji ta hamɓarar da gwamnati ƙasar Guinea-Bissau tare da karɓe mulki, sannan kuma kwanaki biyu da suka gabata aka yi yunƙurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin.
