Daga AISHA ASAS
Kafin na kai ga darasin namu na yau wanda yake da matuƙar tasiri a wannan zamani da muke ciki, zan soma kan shimfiɗa kan ita kanta ɗabi’a ta zagin malamai.
Aya a cikin littafi mai tsarki ta cikin surar Al-An’am, aya ta 153. Allah Maɗaukacin sarki Ya ce, “Kuma lallai wannan ce hanya ta madaidaiciya, ku bi ta, kada ku bi ‘yan hanyoyi, za su rarraba ku daga bin hanyaTa………”
A wani hadisi da ba zan iya tuna ko daga wa ta fito ba, sahabbin ya ce, “Alokacin da manzon Allah yake karanta wannan ayar, yana zaune ne a ƙasa, sai ya sanya wani ƙaramin icce da ke hannunsa ya yi layi tsaye daidai, sai kuma ya yi masa rassa gefe da gefe.” Wannan na nufin yadda kawuna za su rarrabu idan an kauicewa bin hanya guda ɗaya, wadda ita ce daidai, wato hanyar ƙur’ani da hadisi.
Musulunci ya zama addini da ya sha gwagwarmaya kafin kafur sa, idan muna bin tarihi za mu fahimci irin wahala da Annabin Allah da sahabbansa Allah Ya yarda da su suka sha kafin tsayuwar Musulci a matsayin addini mai faɗa a ji kuma mai ‘yanci.
Tun daga lokacin da addinin Musulci ya yi nasara, ya zama a sama, yake kuma tafiya bisa hanya ɗaya kan tsari rin wanda Musulunci ya shar’anta. Wannan ya ba wa Musulunci girma da daraja a idon duniya, kuma ya kasance addini mai faɗa a ji fiye da kowane addini, sakamakon a kullum ƙara samun mabiya yake yi.
A duk inda Musulmi yake to fa ɗan uwan musulmi ne, kamar yadda manzon rahma ya ce, “Al-muslimu akhul Muslim.” Don haka idan ka taɓa musulmi baƙar fata, to ka taɓa Musulmi Balarabe, kuma ka taɓa Musulmi Bature da duk sauran musulmai.
Wannan ya sa ake jin tsoron taɓa musulmi ko Musulunci. Kuma ake ba su girma koda kuwa ba ka son su a zuci. Da wannan ne maƙiya addinin suka shiga bincike da nazarin yadda za a iya karya wannan ƙarfi da Musulunci yake da.
Abinda suka samu tabbaci a binciken nasu kuma suka aminta da shi shi ne, ba za su iya janye wannan girma na musulmai ba, matuƙar ba rarraba kawunansu suka yi ba. Anan wannan ayar da muka ambata ta zama wani jan kunne don gaba da aka yi mana.
Akan wannan ne suka shiga bin hanyoyi don ganin sun karya wannan haɗin kai da ke tsakanin al’ummar musulmai. Kuma sun yi nasara ne ta makamin ‘aƙida’ da suka sanya a tsakaninsu.
Shi’a, Tijjaniya, Salafiya da sauransu duk wata hanya ce ta raba kan musulmai wadda a wannan zamani ta yi matuƙar tasiri, har ta kai wani ɓangare na kallon ɗaya a matsayin wanda ba Musulmi ba.
Yayin da kan musulmai ya rabu, sai darajar su ta faɗi, sai aka fara cin su da yaƙi ɗaya bayan ɗaya ba tare da sun samu tallafi daga sauran ‘yan uwansu musulmai ba, sakamakon kallon da suke masu na ba aƙidarsu ɗaya ba.
Albarkacin aƙida a addinin Musulunci, sai addinin ya kasance maraya, wanda ake cin zarafinsa a duk lokacin da akaga dama, domin an san babu haɗin kai a cikinsa da har za su iya ɗaukar mataki. Duk wani da ya yunƙuro don kare martabarsa, ba zai iya ba don shi kaɗai ne zai yi ba tare da samun goyon bayan saura ba.
Ta dalilin aƙida maƙiya Musulunci ke amfani da ita wurin ɓata sunan addinin ta hanyar kitsa ta’addaci da sunansa. Wanda hakan ke ba su damar yi wa mabiyansa kisan mumuƙe da sunan yaƙi da ta’addanci.
Sanadiyyar rarrabuwa da kaucewa gargaɗin wannan ayar, musulmai suna ɗaga makami ga ‘yan uwansu musulmai, saboda saɓanin fahimta. Suna fatan sharri ga ‘yan uwansu da suka amsa kalma ɗaya don kawai sun barranta daga tasu fahimta.
Ta yaya muke son a tausaya mana bayan ba mu tausayawa kanmu ba. Wallahi da a ce mun tsayu kan abinda Annabi Muhammad (S.A.W) ya gina tare da sahabbai, da Musulunci ba shakka zai zama mai faɗa a ji a duniya. Da babu wanda zai iya cin zarafin ɗaya daga cikin musulmai don kawai yana musulmi, kuma ya zauna lafiya. Da ‘yan uwa musulmai da ke cikin azabtarwa kan kawai sun ce “babu sarki sai Allah” ba su shiga halin da suke ciki ba.
Idan kuwa haka ne, ba wanda za mu yi kuka da shi face kawunanmu. Mu ne muka janyo abinda yake faruwa da mu da hannunmu.
Takai-ta-kawo, a Najeriya, za ka samu matashi da aka haifa a jiya, zai buɗe baki ya yi mummunan zagi ga malamin da ya ɗau shekaru yana ba wa addinin Musulunci kariya, malamin da zai iya sa’ar ubansa ko ma ya yi jika da shi, amma hakan daidai ne, saboda iyaye ko waɗanda yake biya ya nuna hakan a matsayin daidai. Abin takaicin su kansu malaman za su hau mambari su zagi ɗan uwansu malami, su kira shi da sunaye masu muni wai duk da sunan wa’azantarwa.
A yayin da muka shagala da ɓacin malaman da muke da saɓanin fahimta, ya kamata mu yi wa kanmu tambayar shin wa muke kwaikwayo? Idan amsar ita ce Annabi Muhammad (S.A.W), sai mu ƙara da wata tambayar ko abinda muke yi haka ya yi, ko haka sahabbansa suka yi?
Wacce madogara ce za mu riƙe da za mu jingina ta da Annabi a matsayin hujja? Ko a zamanin sahabbai an samu saɓanin fahimta, amma suna abinda ake yi a yanzu?
Duk wannan zage-zagen da muke yi, mun taɓa zama muka tambaye makomar ‘ya’yanmu ta fuskar tarbiyya?
Za mu ci gaba.
