Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Dakta Yakubu Maigida Kachako ya yaba wa cibiyar Khairu Center for Indigenous Knowledge System (KCIKS) bisa yunƙurinta na tattara da adana ilimin gargajiya na kakanni domin amfani a wannan zamani.
Yayin taron da aka gudanar a Jami’ar Khalifah Isyaka Rabi’u (KHAIRUN), Maigida Kachako ya bayyana cewa sama da kashi 80% na mutanen duniya na amfani da magungunan gargajiya, amma Nijeriya ba ta da ingantacciyar hukuma da ke kula da wannan fanni.
Ya ce ilimin gargajiya ya ƙunshi fasaha da hikima, har ma akwai masu iya gano matsalolin lafiya tun daga kuka ko fatar jariri.
Ya ce waɗannan masu ilimi na gargajiya suna da baiwa ta musamman wacce ya kamata gwamnati ta taimaka wajen adanawa da inganta ta.
Shi ma shugaban cibiyar, Farfesa Muhammad Auwal Ibrahim, ya ce sun shafe dogon lokaci suna tattara ilimin gargajiya kamar wazanci, kira, dukanci, rini, farauta da sauran su domin haɗawa da ilimin zamani don amfanin ɗalibai. Ya ce manufarsu ita ce kada ilimin gargajiya ya ɓace.
Ya ƙara da cewa cibiyar na shirin fara samar da kundin rubuce-rubuce da manhajoji domin koyar da ilimin gargajiya ta zamani, tare da kafa dakin karatu na musamman da zai zama tushen bincike. Ya bayyana cewa hakan zai baiwa ɗalibai damar fahimtar asalin al’adunsu da hanyoyin da za su inganta su.
Dakta Kachako ya yi kira ga ma’aikatar lafiya da hukumar NEPC, NAFDAC da masana kimiyya su haɗa kai da cibiyar domin samar da ingantaccen tsari na tabbatar da sahihancin magungunan gargajiya, tare da ba masu sana’ar lasisi don kare mutuncin fannin.
