An kafa cibiyar ‘Mu inganta sana’armu’ don kawar da talauci – Maryam Bichi

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Shugabar cibiyar Mu Inganta Sana’armu, Hajiya Maryam Abbas Abdulkadir Bichi (MB), ta bayyana cewa an kafa cibiyar ne musamman domin habaka sana’o’i da kasuwancin mata ta hanyar amfani da fasahar zamani. 

Ta faɗi haka ne yayin taron shekara–shekara da cibiyar ta shirya a Kano, wanda kamfanoni da masana’antu fiye da 30 suka halarta.

Ta ce an kafa cibiyar ne domin kawar da talauci musamman a tsakanin mata, kasancewar mata sune ginshikin al’umma. Ta jaddada cewa babban kalubalen da mata ke fuskanta shi ne ƙarancin fahimtar amfani da fasahar zamani, musamman injinan da ake sarrafawa cikin harshen Turanci.

MB ta bayyana cewa burinta shi ne cibiyar ta zama babbar cibiyar horar da mata a Nijeriya da ma duniya, domin samar da ci gaban tattalin arziki ga al’umma. 

Ta kuma yaba wa masu buƙata ta musamman da ke fafutukar gudanar da sana’o’insu duk da ƙalubale.

A cewarta, cibiyar za ta ƙara faɗaɗa shirye-shiryenta na horaswa musamman a bangaren kasuwanci ta yanar gizo, ƙirƙira (innoɓation) da hanyoyin samun tallace-tallace ta zamani domin taimaka wa mata su shiga kasuwannin duniya. Ta ce an shirya jawo masu zuba jari domin haɗin gwiwa da cibiyar.

Ta kuma yi kira ga hukumomin gwamnati da masu hannu da shuni da su tallafa wa cibiyar, domin cewar su ne tushen samar da ƙwararrun mata masu zaman kansu da zasu iya dogaro da kansu tare da taimakawa gidajensu da al’ummarsu baki ɗaya.

By ukarofi