An yaba wa gwamnatin Kano kan inganta harkar ilimi

Spread the love

Daga SULAIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

An yaba wa Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa ɗaukar fannin ilimi da muhimmanci ta hanyar gyaran makarantu, samar da kayan koyo da koyarwa da sauran muhimman abubuwan ci gaban ilimi.

Hajiya Rabiya Ahmad Muhammad, Darakta mai kula da ingancin ilimi ta hukumar kula da manyan makarantun sakandare ta kasa, ta bayyana haka yayin rangadin makarantu biyar da hukumar ta gudanar a Kano.

Makarantun sun haɗa da: FGC Kano da GGC Dala da WTC Fanfo da KTC Sabon Gari da Makarantar Al-Azahar (mai zaman kanta)

Ta ce sun duba kayayyakin koyarwa, adadin malamai, ingancin ajujuwa, wuraren cin abinci, da buƙatar ofishin bada shawara ga dalibai.

Kwamitin ya yaba da yadda gwamnatin Kano ke farfaɗo da ilimi, sai dai ya nuna damuwa game da ƙarancin malamai da wasu matsalolin cibiyoyi.

Masu gudanar da makarantun da aka ziyarci sun bayyana farin cikinsu da wannan duba, tare da cewa za su aiwatar da shawarwarin da kwamitin ya bayar domin inganta ilimi.

Manajan makarantar Al-Azahar, Malam Ahmadu Rifa’i ya bayyana cewa samun damar shiga cikin jerin makarantun da aka tantance a Kano babban abu ne na alfahari, tare da cewa shawarwarin hukumar za su taimaka wajen kara inganta makarantar.

By ukarofi