Jihar Kano ta ƙulla alaƙar cinikayya da wasu ƙasashen duniya – Darma

Spread the love

Daga SULAIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

A ƙoƙarinta na bunƙasa tattalin arzikinta da faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga, gwamnatin Jihar Kano ta ƙulla sabuwar yarjejeniyar kasuwanci da wasu ƙasashen duniya, domin ƙara danƙon zumuncin cinikayya da masana’antu. 

ƙasashen da suka shiga cikin yarjejeniyar sun haɗa da Bangladesh, Rwanda, Ghana da wasu manyan ƙasashen duniya masu ƙarfin tattalin arzikin masana’antu.

Shugaban Cibiyar Kasuwanci, Ma’adanai, Masana’antu da Aikin Noma ta Jihar Kano, Ambassador Usman Hassan Darma ne ya bayyana haka yayin ganawarsa da manema labarai bayan rufe bikin bajekolin bana karo na 47.

Darma ya ce wannan shekarar ta samu gagarumar nasara idan aka kwatanta da lokutan baya, domin ƙasashe da dama sun halarci bajakolin, musamman China, Bangladesh, India, Turkey, da ƙasashen Afrika irin su Uganda, Niger, Mali, da Rwanda, inda kowanne ya nuna kayayyakin da yake sarrafawa.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin ƙasashen sun nuna sha’awar ƙulla yarjejeniyar kasuwanci kai tsaye da Jihar Kano, wanda hakan zai ƙara inganta tattalin arzikin jihar.

Ya tabbatar wa ‘yan kasuwa cewa rufe bajekolin bai nufin dakatar da cinikayya ba, domin harkokin kasuwanci za su ci gaba har na tsawon mako guda, domin bai wa waɗanda ba su samu damar halarta ba damar yin ciniki.

Ya kuma yi godiya ga Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf da Kwamishinan Masana’antu da Zuba Jari, Alhaji Shehu Wada Sagagi, bisa irin gudunmawar da suka bayar tun daga shirye-shiryen buɗe kasuwar har zuwa rufeta.

Shugabannin cibiyoyin kasuwanci daga Gombe da Kaduna, Hon. Jalo Ahmad Tanja da Alhaji Faruk Sulaiman (Fas Man), sun nuna farin cikinsu da yadda suka ga cigaba da tsari a wannan bajekoli, tare da cewa suma za su yi koyi da hanyoyin da Kano ta bi don samun nasara.

‘Yan kasuwa da dama sun yaba da yadda aka saurari ƙorafe-ƙorafensu a bana, sannan aka samar da tsaro sosai, saɓanin lokutan baya.

Alhaji Amadu Fala-Fala daga Nijar, wanda ya shafe shekaru kusan 15 yana halartar bajekolin, ya ce wannan shekarar ita ce mafi tsari da kulawa daga bangaren masu gudanarwa.

A wajen rufewa, manyan baki sun halarta, ciki har da Shugaban Marasa Rinjiye a Majalisar Dattawa, Sanata Rufa’i Sani Hanga; Kwamishinan Masana’antu, Hon. Shehu Wada Sagagi; Dr. Rahila Aliyu Mukhtar; da manyan ‘yan kasuwa daga gida da waje.

By ukarofi