Yadda wani gurgu ya ƙera mota a Kano

Spread the love

Daga SULAIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Wani matashin gurgu daga Unguwar Rijiyar Lemo a ƙaramar Hukumar Dala, Ibrahim Abubakar mai shekaru kimanin 32, ya nuna bajintarsa a bikin rufe bajekolin bana ta hanyar gabatar da wata mota da ya ƙera da hannunsa wacce ke ɗaukar mutum huɗu.

Ibrahim ya ce tun yana makaranta yake sha’awar zama injiniya, amma bai samu damar ci gaba da karatu ba bayan kammala sakandare. Ya fara ƙere-ƙere ne tun yana ƙarami, inda yakan gyara kekensa na zuwa makaranta har ya koyi amfani da ƙarafuna da walda.

A cewarsa, motar da ya ƙera tana ɗauke da injin babur suzuki mai gear biyar, tana da gilashi, tayoyi, radio, sannan tana iya ɗaukar mutum huɗu.

Cibiyar Kasuwanci, Masana’antu, Ma’adanai da Aikin Noma ta Jihar Kano, ƙarƙashin Ambassador Usman Hassan Darma, ta karrama shi da kyautar naira miliyan ɗaya domin ƙarfafa masa guiwa.

Ibrahim ya ce wannan tallafi zai ba shi damar cigaba da ƙirƙire-kirkire, sannan ya yi kira ga sauran masu buƙata ta musamman da su fito da baiwar da Allah ya ba su, kada su dogara da bara.

Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta rika tallafa wa mutanen da ke da buƙata ta musamman domin ciyar da su gaba cikin mutunci da sana’ar dogaro da kai.

By ukarofi