Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Kungiyar Gwamnonin Arewa ta kafa asusun magance matsalar tsaro tare da tsara kowacce jiha za ta riƙa ba da Naira biliyan 1 a kowanne wata kamar yadda Blueprint Manhaja ta rawaito.
Gwamnan Nassarawa kuma shugaban kungiyar gwamnonin yankin Arewa ta tsakiya, Abdullahi Sule, ne ya bayyana haka a yayin zaman majalisar zartarwa ta jihar a Lafiya.
A cewar Gwamna Sule, an ɗauki wannan mataki ne a zaman da ƙungiyar gwamnonin Arewa ta yi na ƙarshe a Kaduna.
Ya ce, za a yi amfani da kuɗi ne wajen sayen manyan makamai Ga jami’an tsaro da kuma ɗaukar matasa aikin da nufin tallafa wa jami’an tsaro a yankin.
Ya ce, “daya daga cikin matakan da muka amince da shi ya haɗa da ba da Naira biliyan 1 duk wata ga asusun samar da tsaro. Don haka, dukkan gwamnonin jihohi 19 na Arewa za su haɗa kuɗi Naira biliyan 19 a kowanne wata na tsawon watanni 12. Mun yanke shawarar fuskantar wannan matsalar tsaro domin in ba haka ba, za mu cigaba da magana ne kawai ba tare da ɗaukar mataki ba.”
“Za a yi amfani da kuɗin wajen ayyuka daban-daban da suka haɗa da: sayen kayan aiki da ake buƙata wajen magance tsaro da ɗaukar matasa aiki waɗanda za a bai wa horo a matsayin ‘yan bijilanti.”
Gwamna Suke ya ce, ƙungiyar gwamnonin ta shirya samar da sakatariyarta a Kaduna, tana mai cewa gwamna Uba Sani ya ba da kyautar fili domin gudanar da aikin. Sannan gwamnoni 19 na Arewa sun yarda su ba da gudunmawar Naira miliyan 100 kowannensu domin aza harsashin gina sakatariyar kungiyar ta dindindin.
“Dukkan tarukan da ake yi, ana yi ne a gidan gwamantin Kaduna. Sai dai, gwamnan Kaduna ya ba da kyautar fili a wani wuri inda za mu gina sakatariyarmu. Sannan kowacce jiha za ta ba da Naira miliyan 100 a wannan wata da za a yi amfani da su wajen aza harsashin ginin sakatariyar.”
Sannan ya ce, ƙungiyar ta naɗa Chief Ezekiel Gomos a matsayin darakta-janar na kungiyar gwamnonin Arewa.
Gomos, dai tsohon sakataren gwamnatin jihar Filato, kuma shi ne zai kula da asusun magance matsalar tsaro.
Haka kuma gwamna Sule ya yi ƙarin haske kan matakin dakatar da haƙar ma’adanai da aka cimma a zaman kwanan baya na kungiyar gwamnonin.
Ya ce, dakatarwar ba yana nufin daina haƙar ma’adanai ba ne, dakatarwar ta shafi hana ba da lasisi ga sabbin kamfanonin haƙar ma’adanai har sai an kammala tantance su na haƙiƙa.
Aikin tantancewar na son gano wadanda suka cika ka’ida ne da yin waje da waɗanda suke hakar ba bisa ka’ida ba.
Gwamnan ya ce kasancewar masu haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba ya bai wa ‘yan bindiga mafaka da dalilin gudanar da ayyukansu da haifar da matsalar tsaro.
Ya ba da tabbacin cewa dakatarwar ba an yi ba ne domin hana gwamnatin jihar samun kuɗin shiga ba, sai domin tabbatar da ana gudanar da haƙar ma’adanan bisa tsari da ƙa’ida.
