
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ofishin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro (ONSA), ya tabbatar da ƙarin matsayi ga jami’i Kanal Nurudeen Alowonle Yusuf zuwa Birgediya Janar.
A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannu Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara akan Harkar Tsaro, Nuhu Ribaɗu zuwa ga Shugaban Rundunar Sojoji, ONSA ya kuma tabbatar da cigaba da riƙe jami’in a matsayin mataimaki na musamman, wato ADC ga Shugaba Bola Tinubu.
Hakan na nufin babban jami’in zai cigaba da kasancewa ADC ga Shugaba Tinubu a wani karo tun daga ranar 12 ga watan Disamba, 2025.
NSA, ya kuma taya shi murna tare da masa fatan alkhairi yayin da ya ke fuskantar wani zango a matakin aikinsa.
