Fadar Shugaban Ƙasa ta yi min tayin shiga APC, inji Sanata Natasha

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi ikirarin Fadar Shugaban Ƙasa ta nemi da ta sauya sheƙa zuwa cikin jam’iyyar APC.

Natasha ta bayyana haka ne a wata hira ta Mic On Podcast Seun Okinbaloye a ranar Asabar.

Ta ce, ba za ta bar PDP da nufin komawa APC ba domin tana jin daɗin kwanciyar hankalin da ke cikin jam’iyyar tata.

Sanatar ta kuma ce, ko lokacin da yi aure an yi ta mata tayin tsayawa takara daga Jihar Delta domin mijin da ta aura ɗan can ne.

Ta bayyana cewa, a baya ita mamba ce ta APC ta dan lokaci, amma sakamakon wasu dalilai ya sa ta fice, wanda a cewarta an mata tayi daga fadar da ma wasu daga cikin wasu takwarorinta sanatoci domin ta dawo.

“Ina son wajena. Ina son zaman lafiyata a nan. Na gamsu da jam’iyyata yanzu, don haka ba sai na shiga APC ba”, inji Natasha.

A baya an samu tataɓurza tsakanin ta da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wanda ya samo asali akan wajen zama.

Lamarin da ya janyo Natasha ta zargi jagorancin majalisar da ƙoƙarin tauye ƴancin jinsi wajen mayar sanatoci mata marasa amfani duk da cewa Akpabio ya mayar mata da martani tare da tirjewa akan bin tsarin gudanar da majalisar.

By Babaji