
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar masu shirya fina-finai ta ƙasa MOPPAN, ta miƙa saƙonta na taya murna ga ɗaya daga cikin mambobinta kuma daɗaɗɗen jarumin fina-finan masana’antar Kannywood, Hamisu Lamiɗo Iyantama bisa samun kyautar karramawa ta bajekolin Zuma na 2025.
A wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Shugabanta Shehu Hassan Kano, MOPPAN ta ce hakan ya nuna yadda jarumin ya kasance mai jajircewa, inda ta bada misali da nasarar da fim ɗinsa mai dogon zango na Tsintsiya da ya samu karramawa a 2018.
Ta kuma ce, Iyantama ginshiƙi ne ga ci-gaban harkar fim a Nijeriya musamman ganin yadda yake aiki tuƙuru wajen samar da haɗin kai da shirya lamuran masana’antar bisa tsari.
Don haka ne MOPPAN ta ce tana alfahari da shi da kuma nasarar da ya samu tare da taya shi da iyakansa murna lamarin.

