Gwamnatin Nasarawa da ƙasar Angola za su haɗa hannu don bunƙasa tattalin arzikinsu

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Gwamnan Jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule da takwararsa ta Jihar Bengo a ƙasar Angola wato Dokta Maria Antonia sun rattaɓa hannu a wata yarjejeniya na musamman a tsakaninsu don bunƙasa fannonin aikin noma da ilimi da ma’adanai da sauran su don cigaban jihohin biyu da ma ƙasashen nasu baki ɗaya.

Da yake jawabi a yayin zaman sanya hannun wanda aka gudanar a gidan gwamnatin jihar ta Nasarawa dake Lafiya babban birnin jihar, Gwamna Abdullah Sule ya bayyana cewa tabbas ba shakka yarjejeniyar da zarar aka fara aiwatar da su za su kawo cigaba masu ma’ana a jihohin biyu dama ƙasashen biyu wato Nijeriya da Angola musamman a fannin noma da sauransu.

Gwamna Sule ya ce jihar sa tuni ta gano wasu mahimman fannoni da za su haɗa hannun da gwamnatin Angola don bunnkasa fannonin ta yarjejeniyar.

A cewarsa dole ne a kuma yaba wa hukumomi da suka yi aiki tukuru wajen gano wadannan mahimman fannonin hadin gwiwar tsakanin jihar da takwarar sa ta jihar Bengo ta Angola din.

Ya cigaba da bayana cewa” Kamar yadda maigirma gwamnan Bengo ta bayana ba shakka duka jihohin mu biyu zasu amfana matuka daga juna idan akayi la’akari da dinbin albarkatun kasa da Allah ya albakace mu musamman a fannin aikin noma da wadanda ke kusa da babban birnin tarayya Abuja anan jihar mu ta Nasarawa da sauran albarkatun kasar.” Inji shi.

Tun farko a jawabin ta, gwamnar jihar Bengo ta ƙasar Angola din Dokta Maria Antonia ta bayyana cewa da ita da ayarin ta sun kasance a jihar Nasarawa ne don su sanya hannu a yarjejeniyar na musamman a wadannan mahimman fannonin don cigaba.

Dokta Maria Antonia ta kuma bayyana yarjejeniyar a matsayin abun alfa’ari mai kuma dinbin tarihi sannan ta yaba da mataki da duka bangarorin suka dauka don cimma burin nasu tare musamman a fannin inganta tattalin arzikin gwamnatotin nasu.

A halin da ake ciki Gwamnan na jihar Nasarawa Injiniya Abdullahi Sule tare da takwarar nasa Dr. Maria Antonia sun kuma yo amfani da damar inda suka kaddamar da wasu manyan ayuka a jihar da gwamnatin sa tayi ciki harda babban ginin hedikwayar hukumar tara kidin jihar wato Nasarawa State Inɓestment Deɓelopment Agency (NASIDA) a turance da sauran su duk ayayin ziyarar gwamnar Bengo ɗin ta ƙasar Angola.

By ukarofi