Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa mai Zaman Kanta (ICPC) ta sanar da cewa ta samu nasarar ƙwato kadarori da kuɗaɗe da suka kai naira biliyan 37.44 da kuma dalar Amurka miliyan 2.353 a cikin shekarar 2025, adadin da ake ganin yana daga cikin mafi girma da hukumar ta taɓa cimmawa a shekara guda.
Shugaban hukumar, Dakta Musa Adamu Aliyu, SAN, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin taron ƙarshen shekara na ICPC, wanda ya haɗa da bankwana ga ma’aikatan da suka yi ritaya da kuma bikin karrama ma’aikatan da suka nuna kwazo a aiki.
Aliyu ya bayyana shekarar 2025 a matsayin muhimmiyar shekara da aka samu manyan nasarori a ɓangarorin bincike, rigakafi da wayar da kan jama’a.
Yayin da yake nazarin ayyukan hukumar, shugaban ICPC ya ce an binciki shari’o’i 263 a cikin shekarar, adadin da ya wuce burin da aka sanya na shari’o’i 250.
Haka kuma, ya ce an kai shari’o’i 61 kotu, inda aka samu kaso 55.74 na hukuncin samun laifi. A cewarsa, wannan ya nuna ƙaruwar tasiri da jajircewar hukumar wajen ganin an hukunta masu aikata laifukan cin hanci.
Daga cikin manyan nasarorin da aka cimma, Aliyu ya ambaci hukuncin da aka yanke wa Farfesa Cyril Ndifon na University of Calabar, wanda kotu ta yankewa hukuncin ɗaurin shekaru biyar bisa laifukan cin zarafin ɗalibai ta hanyar lalata da kuma amfani da kafafen sadarwa wajen cin zarafi.
Shugaban ICPC ya ce hukuncin ya aikewa da saƙo mai ƙarfi cewa hukumar ba za ta lamunci duk wani nau’i na cin zarafin ofis ko amfani da iko ba bisa ƙa’ida.
Aliyu ya kuma bayyana gagarumin aikin rigakafi da hukumar ta gudanar a ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati daban-daban.
Ya ce an tantance hukumomi 344 ta hanyar amfani da ma’aunin kimanta ladabi da gaskiya, tare da aiwatar da ayyukan sa ido kan cin hanci guda 66 da kuma bibiyar ayyukan gwamnati 1,490 a faɗin ƙasar.
Bugu da ƙari, an kammala nazarin tsarin aiki da tantance haɗarin cin hanci a hukumomi 12, domin rage guraben da ke bai wa cin hanci damar shiga cikin tsarin gwamnati.
A ɓangaren wayar da kan jama’a, shugaban ICPC ya ce sama da ‘yan Nujeriya 235,000 suka amfana daga shirye-shiryen faɗakarwa 644 da aka gudanar, yayin da aka samu mu’amalar dijital har kusan miliyan 3.5. Ya kara da cewa an kafa ƙungiyoyin yaƙi da cin hanci 86 a makarantu da al’umma, tare da horas da mutane 2,707 a makarantar horaswa ta ICPC.
Hukumar ta kuma faɗaɗa haɗin gwiwa da sauran ƙungiyoyi, inda ta ƙaddamar da ayyukan haɗin gwiwa 15, yayin da ƙungiyoyin fararen hula suka aiwatar da shirye-shirye 57 domin tallafa wa yunkurin yawi da cin hanci.
A ƙarshen taron, an karrama ma’aikatan da suka yi ritaya bisa jajircewa, kwarewa da dogon hidimar da suka yi wa ƙasa.
