Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata ƙungiya mai zaman kanta suna ‘Rights for All International’ RAI ta shigar da ƙara a gaban Kotun Tarayya da ke Abuja, tana neman a yi bincike game da rikicin Aliko Dangote da Farouk Ahmed.
A ƙarar da RAI ta shigar, lauyan ƙungiyar Okere Nnamdi ya buƙaci kotu ta ayyana cewa Farouk Ahmed ya aikata laifin karɓar kuɗi daga hannun wasu ba bisa ƙa’ida ba.
Idan dai ba a manta ba, Alhaji Aliko Dangote na zargin Farouk Ahmed, tsohon shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur na Tsakiya da ƙasa (NMDPRA), bisa zargin rashin gaskiya da kuma yin amfani da muƙaminsa wajen amfanin kansa.
ƙungiyar ta shigar da ƙarar ne a ranar Laraba, jim kaɗan bayan ɓullar labarin cewa Farouk Ahmed da shugaban Hukumar NUPRC, Gbenga Komolafe, sun yi murabus daga muƙamansu.
Rahoton ya bayyana cewa ƙarar ta biyo bayan zarge-zargen da Aliko Dangote, shugaban rukunin kamfanin Dangote, ya yi wa Farouk Ahmed.
Dangote ya zargi Ahmed da lalata tattalin arziki, yana cewa ayyukansa na hana ci gaban harkar tace man fetur a cikin gida.
A wani taron manema labarai da ya gudanar a Matatar Dangote, Dangote ya ce shugabancin NMDPRA na haɗa baki da ‘yan kasuwar ƙetare da masu shigo da man fetur mara kyau.
Dangote ya kuma zargi Farouk Ahmed da rayuwa fiye da ƙarfin albashinsa, yana mai cewa ‘ya’yansa huɗu suna karatu a makarantu masu tsada a Switzerland.
A cewarsa, kuɗin karatun da kula da su ya kai dala miliyan 7 abin da ya haifar da tambayoyi kan tushen kuɗin da ya samo wajen biyan kuɗin.
A ranar Talata, Dangote ya kai koken hukuma ga ICPC ta hannun lauyansa, Ogwu Onoja, SAN, inda ya buƙaci a kama, a bincike, tare da gurfanar da Ahmed.
ƙungiyar ta kuma buƙaci kotu ta umarci Shugaba Tinubu da ya dakatar da Farouk Ahmed nan take, tare da tilasta wa hukumomin yaƙi da rashawa irin su ICPC, EFCC da CCB su gudanar da bincike da kai shi kotu.
RAI ta ce, ta shigar da ƙara ne don kare muradin jama’a, tana jaddada cewa kundin tsarin mulkin Nijeriya ya haramta cin hanci da rashawa.
ƙungiyar ta ce, ‘yan Nijeriya na ci gaba da shan wahala sakamakon cire tallafin man fetur, wanda ta ce asalin matsalar shi ne cin hanci da rashawa a ɓangaren mai.
