Naira ta ƙara farfaɗo a kasuwar canji

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD

Darajar Naira ta rufe mako cikin ƙarfi a ranar Juma’a, bayan ta samu ƙarin Naira 1.65 kan dalar Amurka a kasuwar canji ta hukuma, inda aka sayar da ita kan N1,454.41.

Bayanan da Babban Bankin Nijeriya ya fitar ta shafinsa na hukuma sun nuna cewa wannan sauyin ya wakilci ƙarin kashi 0.11 cikin 100 idan aka kwatanta da ranar Alhamis, lokacin da Naira ta tsaya a kan N1,456.06 a kowace dala.

A farkon makon cinikayyar, Naira ta fuskanci ɗan raguwar daraja, inda aka samu asara kaɗan-kazan a tsawon makon. A ranar Laraba, an sayar da kuɗin a kan N1,455.38, abin da ya nuna cewa kasuwar na cikin yanayin da ba a samu manyan sauye-sauye ba.

A ranakun Litinin da Talata kuwa, Naira ta yi ciniki a kan N1,451.86 da kuma N1,454.38 bi da bi, kafin daga bisani ta ɗan farfaɗo a ƙarshen makon. Masana harkar kuɗo na ganin cewa wannan ɗan ƙarfafa darajar Naira na iya nuna ƙoƙarin da ake yi wajen daidaita kasuwar musayar kuɗaɗe, duk da matsin lambar da tattalin arziƙi ke fuskanta.

Sai dai duk da wannan ƙananan nasara, masu lura da kasuwa na jaddada cewa har yanzu ana buƙatar tsare-tsare masu ɗorewa domin tabbatar da kwanciyar hankali da inganta darajar Naira a dogon lokaci, musamman a gaban ƙalubalen hauhawar farashi da buƙatar dalar waje.

By ukarofi