Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da harin Amurka akan ƴan ta’addar ISIS a Nijeriya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da haɗin-gwiwar tsaro da leƙen asiri tsakanin Nijeriya da Amurka biyo bayan harin maɓoyar ƴan ta’adda a yankin Arewa maso yammacin Nijeriya da Amurka ta kai a yankin jihar Sakkwato a daren Juma’a.

A cewar Ma’aikatar Harkokin Waje wannan mataki ya haifar da samun ƙarin nasarori a yunkurin kai hare-haren jiragen sama da suka yi a wasu sansanonin ƴan ta’adda a yankin.

A wata sanarwa da Kakakin Ma’aikatar, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ya fitar a yau Juma’a, an bayyana cewa haɗin-gwiwar tsaron ya ƙunshi musayar bayanan sirri, dabarun tsaro, da sauran nau’ikan goyon baya da suka dace da ka’idojin ƙasa-da-ƙasa tare da mutunta ikon ɓangarorin biyu.

Ta ce, duk wani yaƙi da ta’addanci a Najeriya yana gudana ne da nufin kare rayukan fararen hula, tabbatar da haɗin kan ƙasa da kuma kiyaye mutuncin kowane dan ƙasa ba tare da la’akari da addini ko ƙabila ba.

Don haka Gwamnatin Tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu take cigaba da amfani da hanyoyin diflomasiyya da tsaro tare da abokan hulɗa domin tarwatsa ƴan ta’adda, katse hanyoyin samun kuɗaɗensu da kuma hana su samun sababbin maɓoya gami da ƙarfafa cibiyoyin tsaron gida da kayan leƙen asiri.

A ƙarshe, ma’aikatar ta ce za ta cigaba da wayar da kan jama’a da sanar da al’umma duk wani ci-gaba da aka samu a yaƙi da ta’addanci ta hanyar kafafen watsa labarai da gwamnati ta amince da su a hukumance.

By Babaji