Dalilina na ƙin goyon bayan Tinubu a 2027 – Makinde

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana dalilan da suka sa ba zai mara wa Shugaba Bola Tinubu baya a zaɓen 2027 ba, yana mai bayyana yadda rarrabuwar kai ke ƙara ta’azzara a cikin jam’iyyar PDP.

Makinde ya yi wannan bayani ne a yayin wata tattaunawa da manema labarai a Ibadan, babban birnin jihar, inda ya waiwayi farkon rayuwarsa ta kasuwanci.

Ya ce, yana da shekara 29 kacal lokacin da ya samu babbar kwangilarsa ta farko daga kamfanin Mobil, wadda darajarta ta kai dala miliyan ɗaya, lamarin da ya ce ya zama ginshiƙin nasarorinsa a kasuwanci da siyasa.

Gwamnan ya ƙara da cewa, a wancan lokaci Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, wataƙila yana daf da kammala makarantar lauya ko kuma ya kammala kenan.

A cewarsa, wannan kwangila ta sauya masa rayuwa tare da buɗe masa ƙofa zuwa manyan damarmaki a fagen kasuwanci da siyasa.

Da yake magana kan saɓanin siyasa tsakaninsa da Wike, Makinde ya ce rikicin ya fara fitowa fili ne a wani taro da ya hada su da Shugaba Bola Tinubu, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila, da wasu manyan jami’ai. A nan ne, inji shi, Wike ya faɗa wa Shugaban ƙasa cewa zai “riƙe PDP” domin taimaka masa a zaɓen 2027, magana da ta ba shi mamaki sosai.

Makinde ya ce, Shugaban ƙasa bai buƙaci Wike ya ɗauki wannan mataki ba, sai dai shi ne ya yi hakan da kansa.

Ya ƙara da cewa, ko da yake Wike yana da ‘yancin mara wa Tinubu baya, su ma waɗanda ke son kare dimokuraɗiyyar jam’iyyu da rayuwar PDP suna da ‘yancin yanke nasu shawarar.

Gwamnan ya bayyana cewa duk da ƙoƙarinsa na tattaunawa da Wike domin a samu fahimta, ba a samu sauyi ba, lamarin da ya sa ya ɗauki matsaya mai tsauri.

Ya ce daga wannan lokaci ya yanke shawarar ba zai kasance cikin wannan tsari ba, yana mai jaddada cewa kowa na da ‘yancin zaɓar wanda zai mara wa baya da rawar da zai taka a zaɓen 2027.

Maganganun Makinde sun ƙara fito da girman rabuwar kai a cikin PDP, inda ake ganin ɓangarori biyu masu ƙarfi sun fara ɗaukar salo. ɓangare ɗaya na ƙarƙashin Wike na nuna kusanci da Shugaba Tinubu, yayin da bangare na biyu ƙarƙashin Makinde ke kira ga ‘yancin jam’iyya da kare tsarin dimokuraɗiyyar jam’iyyu masu yawa gabanin zaɓen 2027.

By ukarofi