Yadda sanatoci biyu da ’yan majalisa shida masu biyayya ga Wike suka koma APC

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Yanayin siyasar Jihar Ribas na ci gaba da sauya salo bayan da sanatoci biyu da mambobin Majalisar Wakilai shida suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC a hukumance.

Sanatocin da suka sauya sheƙa su ne Sanata Allwell Onyesoh mai wakiltar Ribas ta Gabas da Sanata Barinada Mpigi daga Ribas ta Kudu maso Gabas.

An sanar da sauyin jam’iyyar ne a yayin zaman Majalisar Dattawa, inda aka dakatar da dokokin majalisar domin bai wa Sakataran APC na ƙasa, Ajibola Basiru, da wasu manyan jam’iyyar damar shiga zauren domin shaida lamarin.

Sanatocin biyu, da ake kallon su a matsayin amintattun tsohon gwamnan Ribas kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, sun bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da ke addabar PDP ne suka tilasta musu yanke wannan shawara.

Da wannan sauyi, jam’iyyar APC ta ƙara ƙarfafa rinjayenta a Majalisar Dattawa, inda yawan sanatocinta ya haura 78, lamarin da ya ba ta cikakken rinjaye a majalisar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, shi ma ke ci gaba da kusantar APC.

Duk da ƙorafe-ƙorafen da ke tashi kan yawaitar sauya sheƙa zuwa APC, tare da fargabar cewa Nijeriya na iya koma wa jam’iyya guda, shugabannin Majalisar Dattawa sun jaddada cewa dimokiraɗiyya na ci gaba da tafiya yadda ya dace.

Jagoran Majalisar Dattawa, Opeyemi Bamidele, ya ce karuwar ’yan majalisa a APC ba zai janyo koma bayan dimokiraɗiyya ba.

Ya tabbatar da cewa APC na da alhakin kare tsarin dimokiraɗiyya tare da yin aiki da jam’iyyun adawa domin amfanin al’umma, musamman a fannonin samar da abinci da inganta lafiyar jama’a.

Shi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bukaci APC ta tabbatar da adalci da dimokiraɗiyya a cikin gidanta, yana mai cewa duk wanda ya shiga jam’iyyar zai samu dama da adalci. Ya kuma nuna tausayinsa ga jam’iyyun adawa, yana kira gare su da su warware matsalolin cikin gida da ke damunsu.

A Majalisar Wakilai kuwa, ’yan majalisa shida daga Ribas, masu biyayya ga Wike, sun fice daga PDP zuwa APC. Sun haɗa da Dumnamere Robinson Dekor daga Khana/Gokana, Solomon Bob daga Abua/Odual da gabashin Ahoada, Hart Cyril daga Degema/Bonny, Victor Obuzor daga Ahoada West/Ogba-Egbema/Ndoni, Blessing Amadi daga Fatakwal ta II, da Feliɗ Nweke daga Eleme/Oyigbo/Tai.

Sauyin sheƙar da waɗannan ’yan majalisa suka yi na ƙara nuna yadda siyasar Ribas ke shiga wani sabon salo, tare da tasiri kai tsaye ga ƙarfin jam’iyyu a matakin ƙasa.

By ukarofi