Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Bassey Eno, ya bayyana wani sashe mai raɗaɗi amma mai ilmantarwa na rayuwarsa, inda ya ce rasuwar mahaifinsa ta jefa iyalinsu cikin mawuyacin hali, lamarin da ya tilasta masa yin sayar da lemun kwalba a titunan Legas domin taimaka wa mahaifiyarsa.
Gwamna Eno ya bayyana haka ne yayin da yake gabatar da jawabin taron kammala karatu na karo na bakwai a Jami’ar Mountain Top da ke Ibafo, Jihar Ogun.
A cewarsa, mahaifinsa jami’in ’yan sanda ne da ya rasu yana bakin aiki, lamarin da ya sauya alƙiblar rayuwar iyalinsu baki ɗaya, tare da tilasta masa fuskantar ƙalubalen rayuwa tun yana ƙarami.
Ya ce, bayan rasuwar mahaifinsa, rayuwa ta yi tsauri ƙwarai, inda ya riƙa sayar da lemun kwalba da sauran kayan sha a titunan Legas domin tallafa wa mahaifiyarsa, duk da kasancewarsa babban jami’in ɗalibai a Makarantar Victory High School a wancan lokaci.
A cewarsa, wannan gogayya ce ta musamman da ta gina masa jajircewa, ƙoƙari da kuma hangen nesa na kasuwanci.
Gwamnan ya bayyana cewa wahalhalun da ya fuskanta a ƙuruciya ne suka share masa fagen samun nasara daga baya a harkar kasuwanci, inda ya kafa ɗaya daga cikin manyan kamfanonin otel-otel a Jihar Akwa Ibom, kafin daga bisani ya tsunduma cikin harkar siyasa da hidimar jama’a.
Da yake jawabi ga ɗaliban da suka kammala karatu, Gwamna Eno ya ƙarfafa musu gwiwa da su yi mafarki mai girma, su rungumi sabbin tunani, tare da jajircewa wajen aiki tuƙuru.
Ya gargaɗe su da su guji al’adar neman nasara cikin gaggawa ba tare da ƙoƙari ba, yana mai cewa yawancin masu wannan tunani sukan faɗi a hanya.
A wata sanarwa da Fadar Gwamnatin Akwa Ibom ta fitar, Eno ya jaddada cewa ci gaba na gaskiya yana buƙatar ladabi, ƙwarewa, jajircewa da kuma dogaro ga Allah.
Ya bayyana cewa a wannan zamani da fasaha ke sauya komai, matasa su zama masu ƙarfin tunani da iya daidaita kansu da sabbin yanayi.
Ya ce, yawancin matasa a yau na nuna son kai da gaggawar samun riba ba tare da ƙoƙari ba, yana mai jan hankalinsu da cewa irin wannan hanya galibi na kaiwa ga takaici da rushewa.
Ya kuma danganta nasararsa da gaskiya, taimakon daga Allah da kuma taimakon mutanen da ya kira “masu taimakon ƙaddara.”
Gwamnan ya ce duk da matsayinsa a yau a matsayin fasto, ɗan kasuwa da kuma gwamna, har yanzu yana alfahari da ƙanƙantar farkon rayuwarsa, yana mai cewa ladabi da tausayi ga marasa ƙarfi su ne ginshiƙan halayensa.
A nasa jawabin, Shugaban Cocin Mountain of Fire and Miracles Ministries kuma Shugaban Jami’ar Mountain Top, Farfesa Daniel Kolawole Olukoya, ya yaba wa Gwamna Eno bisa jawabin da ya ce ya cika da darussa masu ƙarfi da kuma jagoranci na ƙima.
Shi ma Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Elijah Adebowale Ayolabi, ya bayyana jawabin a matsayin mai motsa tunani da tasiri mai zurfi ga matasan da ke shirin fuskantar rayuwar aiki.
