Ajayi ya sha alwashin kyautata dangantakar DSS da ’yan jarida

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Daraktan Janar na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta ƙasa (DSS), Oluwatosin Adeola Ajayi, ya sha alwashin samar da yanayi mai sauƙi da adalci da zai bai wa ’yan jarida damar gudanar da aikinsu cikin ’yanci da kariya a Nijeriya.

Ajayi ya bayyana hakan ne a wata wasiƙa mai kwanan wata 19 ga Disamba, 2025, wadda ya sanya wa hannu da kansa, inda ya aika wa Shugaban Cibiyar ƙasa da ƙasa ta ‘Yan Jarida (IPI) reshen Nijeriya, Musikilu Mojeed.

Wasiƙar ta zo ne a matsayin martani ga lambar yabo ta karramawa da ƙungiyar ta ba shi bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen kare ‘yancin ‘yan jarida.

Daraktan Janar na DSS ya ce zai ci gaba da zama gaba wajen tabbatar da adalci ga ‘yan jarida tare da samar da yanayi mai kyau da zai ba su damar yin ayyukan su, bisa tsarin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke bi na kare duk ‘yan Nijeriya ba tare da la’akari da ƙabila, addini ko sana’a ba.

Ya kuma bayyana cewa ya riga ya fara tuntuba da shugabannin sauran hukumomin tsaro domin jaddada muhimmancin kare lafiyar ‘yan jarida da mutunta aikinsu a faɗin ƙasar nan.

A cewarsa, kare ‘yancin faɗin albarkacin baki da aikin jarida abu ne mai muhimmanci ga dimokiraɗiyya da zaman lafiya.

Daraktan Janar ɗin ya yaba wa IPI Nijeriya bisa jajircewarta wajen ƙarfafa rahotanni masu tsari, daidaito da sanin ya kamata, musamman kan batutuwan tsaro da ci gaban ƙasa. Ya kuma jaddada aniyarsa ta ci gaba da haɗa hannu da ƙungiyar da mambobinta domin gina dangantaka mai amfani ga kowa.

A wata sanarwa da Sakataren IPI Nijeriya, Ahmed I. Shekarau, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta tunatar da cewa an mika wa Ajayi lambar yabo ta karramawa ne a yayin taron shekara-shekara na IPI Nijeriya na 2025 da aka gudanar a Abuja a ranar 2 ga Disamba, domin yaba wa da nuna goyon baya ga tsayuwarsa kan kare ‘yancin ‘yan jarida da lafiyarsu.

Sanarwar ta ce, tun bayan naɗa Ajayi a matsayin Daraktan Janar na DSS a ƙarshen watan Agusta, 2024, an samu sauyi a yadda hukumar ke mu’amala da kafafen watsa labarai, inda aka ragu da tsangwama, barazana da tsare ‘yan jarida ba tare da hujja ba. A maimakon haka, ana warware matsaloli ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna.

IPI Nujeriya ta kawo misalai da dama na irin wannan sauyi, ciki har da gaggawar umarnin sakin wani zan jarida da aka tsare a Legas a farkon naɗin Ajayi, da kuma magance matsalar tsangwamar da wani babban jami’in kafar yaca labarai ya sha tsawon shekaru a iyakokin ƙasa. 

Haka kuma, ƙungiyar ta yabawa matakin da Daraktan Janar ya ɗauka na hukunta jami’an DSS da suka tsare ‘yan jarida biyu a Jos tare da umarnin ba su haƙuri a bainar jama’a.

ƙungiyar ta ce, ta yi wannan yabo ne ba wai kawai domin ƙarfafa Ajayi ya ci gaba da kyawawan ayyukan ba, har ma domin zama abin koyi ga sauran jami’an gwamnati da hukumomi wajen mutunta ‘yancin ‘yan jarida da dokokin dimokiraɗiyya.

By ukarofi