Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mai ba Shugaban ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, ya bayyana cewa ingantaccen bayanan sirri da kuma jajircewar Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tare da haɗin gwiwar abokan hulɗa na ƙasashen waje, ne suka kai ga nasarar ceto ragowar yara 130 na makarantar Katolika da aka yi garkuwa da su a Jihar Neja.
Ribadu ya bayyana hakan ne a ranar Litinin ta bakin Janar Garba Adamu Laka, yayin tarbar yaran da aka ceto a Fadar Gwamnatin Jihar Neja da ke Minna.
Ya ce haɗin kai da tsare-tsaren sirri na Hukumar DSS, Sojojin ƙasa, ’Yan Sanda da sauran hukumomin tsaro, tare da goyon bayan abokan hulɗa na ƙetare, ne suka tabbatar da sakin yaran cikin ƙoshin lafiya.
Janar Laka, wanda shi ne Babban Mai Gudanar da Ayyukan Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), ya jaddada cewa wannan nasara ta samo asali ne daga umarnin Shugaban ƙasa, wanda shi ne Babban Kwamandan Askarawan Nijeriya.
Ya ce ofishin NSA ya jagoranci aikin ceto cikin tsari da kulawa ta musamman, lamarin da ya haifar da nasarar dawo da yaran ba tare da an cutar da su ba.
“Wannan ceto wata babbar nasara ce da ta samo asali daga umarnin Shugaban ƙasa da kuma jajircewar hukumomin tsaro, ciki har da DSS, Sojoji, ’Yan Sanda da abokan hulɗa na ƙasashen waje,” inji Laka.
Yaran da aka ceto sun iso Fadar Gwamnatin Neja da misalin ƙarfe 1:30 na rana a cikin manyan motocin bas guda shida, tare da tsauraran matakan tsaro da suka haɗa da motocin sulke da na kariya daga harsasai na DSS da Rundunar Sojin ƙasa.
ɗaya daga cikin malamai mata da aka yi garkuwa da su tare da yaran, ta bayyana farin cikinta, tana mai cewa ba ta taɓa tsammanin za ta yi bukin Kirsimeti a gida ba. “Na yi matuƙar farin ciki. Ban yi tsammanin zan yi Kirsimeti a gida ba,” inji ta cikin jimami da godiya.
Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya tarbi yaran da kansa, inda ya gode wa Allah da kuma Shugaban ƙasa Tinubu bisa dawowar yaran cikin ƙoshin lafiya. Ya ce wannan rana ta kasance ta farin ciki ga iyaye da al’ummar jihar baki ɗaya, kasancewar yaran za su yi bukukuwan Kirsimeti tare da iyalansu.
A wani ɓangare kuma, ƙungiyar NSCI ta yaba wa Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, da ƙaramin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, kan kama shahararren jagoran ’yan fashi da dillalin makamai, Bako Wurgi. ƙungiyar ta bayyana cewa kamen nasa wata babbar nasara ce a yaƙi da ’yan fashi da ta’addanci, musamman a Arewa maso Yamma.
NSCI ta ce, ingantaccen haɗin gwiwa, amfani da bayanan sirri da kuma dabarun tsaro na shugabannin soji na yanzu sun kara wa jama’a ƙwarin gwiwa game da ikon gwamnati na dawo da zaman lafiya.
Ta kuma jaddada muhimmancin ci gaba da bai wa hukumomin tsaro goyon baya, tare da haɗa dabarun tsaro da shirye-shiryen bunƙasa tattalin arziki da ilimi domin hana matasa faɗawa harkar laifi.
