Gyara fasalin haraji na iya tauye tsarin mulki – Farfesa Yadudu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Farfesan shari’a, Auwalu H. Yadudu, ya magantu kan abin da ya bayyana a matsayin wata barazana ga tsarin mulkin dimokurɗiyya, biyo bayan gano bambance-bambance tsakanin dokokin haraji da Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai suka amince da su, da kuma nau’ikan dokokin da gwamnatin tarayya ta wallafa a Jaridar Gwamnati (Gazette).

A cikin wani tsokaci mai zurfi, Farfesa Yadudu ya ce bayan duba wata takarda da ke bayyana saɓanin da ke tsakanin dokokin da Majalisar Tarayya ta zartar da kuma irin su da aka wallafa daga baya, ya kai ga wani ƙarshe mai tsanani cewa akwai yiwuwar wasu ɓangarori a ɓangaren zartarwa sun sauya dokokin ba tare da izinin majalisa ba, domin aiwatar da shirin gyaran haraji ta hanyar umarnin gwamnati.

Tsokacin nasa ya biyo bayan ƙudirin da ɗan Majalisar Wakilai, Abdussamad Dasuki mai wakiltar Kebbe/Tambuwal a Jihar Sokoto, ya gabatar a zaman majalisar ranar Laraba.

Dasuki ya zargi gwamnatin tarayya da tauye hurumin majalisa, inda ya ce tanade-tanaden dokokin haraji huɗu da majalisa ta tattauna, ta daidaita tare da amincewa da su, sun bambanta da abin da aka wallafa a jaridar hukuma.

Farfesa Yadudu ya ce idan aka tabbatar da irin waɗannan sauye-sauye, hakan na girgiza tushen tsarin mulki.

A cewarsa, “Ta yaya za a yi a canja dokoki da aka tattauna a bainar jama’a, aka yi sauraron ra’ayoyin jama’a a kansu, sannan majalisa ta amince da su, amma daga baya a cire wasu tanade-tanade ko a saka sabbi gaba ɗaya?”

Ya kawo misalai daga Dokar Gudanar da Haraji ta ƙasa, inda ya ce an samu sauye-sauye a tanade-tanaden da suka shafi harajin man fetur da na VAT, waɗanda suka rushe matsayar da majalisa ta cimma tare da haifar da rikice-rikicen doka.

Ya kuma nuna wani tanadi a sigar da aka wallafa wanda ya wajabta amfani da dalar Amurka kawai wajen lissafin haraji, saɓanin dokar da majalisa ta amince da ita wadda ta yarda a yi lissafi da kowace kuɗi gwargwadon yanayin mu’amala.

A cewarsa, dokar da aka wallafa ta kuma ƙara wani sharaɗi da ke tilasta mai biyan haraji ya biya kashi 20 cikin 100 na harajin da ake jayayya a kansa kafin ya shigar da ƙara, alhali wannan bai kasance cikin dokar da majalisa ta zartar ba. Ya bayyana irin wannan tanadi a matsayin mai yiwuwa ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

Yadudu ya kuma soki tanade-tanaden da ke bai wa hukumomin haraji ikon kwace kuɗi ba tare da umarnin kotu ba, yana mai gargaɗin cewa hakan na tauye adalci da rawar da ɓangaren shari’a ke takawa.

Ya ce dokar da majalisa ta amince da ita ta tanadi sai da umarnin kotu, amma sigar da aka wallafa ta cire wannan sharaɗi ga wasu hukumomi.

Ya ce waɗannan misalai kaɗan ne daga cikin abubuwan da aka gano, yana mai jaddada cewa akwai yiyuwar ƙarin saɓani a sauran dokokin gyaran haraji. A cewarsa, wannan lamari ya lalata amincin ɗaukacin shirin gyaran haraji tare da ƙara raunana amincewar jama’a ga gwamnati.

Farfesa Yadudu ya buƙaci Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai da su gudanar da bincike a bayyane domin gano wanda ya ba da umarnin sauya dokokin da kuma yadda aka aiwatar da hakan.

Ya kuma yi tambaya kan dacewar fara aiwatar da dokokin daga ranar 1 ga Janairu, 2026, yana mai gargaɗin cewa aiwatar da dokoki da ake zargin rashin halaccinsu zai jefa gwamnati cikin rikice-rikicen shari’a.

A ƙarshe, ya ce ci gaba da tafiya da dokokin a wannan yanayi na iya zama ƙarfafa tauye ikon majalisa, yana mai kira da a dakata har sai an warware duk wata shakka.

By ukarofi