Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Sojojin rundunar Forward Operating Base (FOB) Wukari, karkashin rundunar 6 Brigade na Sojojin Nijeriya /Sashe na 3 na rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS), sun cafke wani shahararre kuma ƙasurgumin jagoran ‘yan bindiga a ƙaramar Hukumar Ukum ta Jihar Benue.
A wata sanarwa da Umar Muhammad, mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar, ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cafke jagoran ‘yan bindigar a matsayin gagarumin nasarar aiki ga sojoji.
A cewarsa, cafke fitaccen jagoran ‘yan bindigar da ke da alhakin sace-sace da fashi da makami da dama a kan hanyar Benue–Taraba babban ci gaba ne ga rundunar.
Ya ce, “An gudanar da cafke mutumin ne a ranar 22 ga Disamba, 2025, yayin wani takamaiman aiki da aka gina bisa sahihan bayanan sirri a yankin ɓaase, Karamar Hukumar Ukum ta Jihar Benue.
“Wannan aiki ya kai ga cafke Fidelis Gayama, wani babban wanda ake nema ruwa a jallo da hukumomin tsaro.”
Ya ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa wanda ake zargin yana da alaka ta kusa da Aka Dogo, wani jagoran kungiyar dauke da makamai da ake nema.
“Yanzu haka wanda ake zargin yana hannun sojoji, kuma za a mika shi ga hukumar da ta dace domin cikakken bincike da gurfanarwa bisa ga dokokin da ke aiki,” inji shi.
Kwamandan 6 Brigade, Kingsley Uwa, ya yaba wa sojojin bisa kwarewarsu, ladabi da kuma daidaiton aiki.
Ya bayyana cafke jagoran ‘yan bindigar a matsayin babban koma-baya ga ƙungiyoyin masu aikata laifuka da ke aiki a yankin.
Mr Uwa ya sake jaddada ƙudurin rundunar na ci gaba da kai hare-haren kawar da masu laifi tare da tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
Haka kuma, Kwamandan ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai a kan lokaci ga hukumomin tsaro domin tallafa wa kokarin tabbatar da tsaro da ake yi.
