NIPC ta janyo masu zuba jari 3,016 a tsakiyar 2025

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Talla da Jawo Hannun Jari ta ƙasa (NIPC) ta bayyana cewa ta jawo masu zuba jari 3,016 kai tsaye a tsakiyar shekarar 2025, sakamakon ayyukan zuba jari da aka aiwatar a ɓangarorin masana’antu, fasahar sadarwa (ICT), sarrafa amfanin gona da lantarki.

Babbar Darakta kuma Shugabar Hukumar, Aisha Rimi, ta bayyana hakan yayin ganawar manema labarai da hukumar ta shirya, inda ta ce manyan nasarorin zangon sun haɗa da karɓar tambayoyin masu zuba jari 713, taimaka wa rijistar kasuwanci 71, amincewa da izinin kwararru 186, tare da bai wa kamfanoni 17 tallafin PSI.

A cewarta, zangon biyu ya mayar da hankali kan juya alƙawuran zuba jari zuwa ayyuka na zahiri, inganta dandamalin fasahar, da kuma ƙarfafa shirye-shiryen jawo jari a matakin jihohi. Ta bayyana cewa a zangon farko na 2025, NIPC ta shimfiɗa tubali mai ƙarfi ta hanyar faɗaɗa ‘National Inɓestment Certification Programme for States’ (NICPS), ci gaba da kula da PSI, da inganta ayyukan ‘One-Stop Inɓestment Centre’ (OSIC).

Hukumar ta ce, ta samu nasara wajen kammala rijistar kasuwanci cikin awanni 48, inganta martani ga tambayoyin masu zuba jari, da kuma taimaka wa kafa kusan kamfanoni 100. Haka kuma, an samu sauƙi a tsarin biza-da-zuwa-da-isowa da izinin aiki, tare da ƙarfafa hulɗa da jihohi da manufofi domin shimfiɗa sabbin zuba jari nan gaba.

Rimi ta ƙara da cewa, NIPC ta kara haskaka Nujeriya a manyan taruka na ƙasa da ƙasa da suka haɗa da tattaunawar Brazil–Nijeriya, Sweden–Nijeriya, ƙumgiyar CEO ta Afrika da ƙungiyar BRICS ta Mata, inda aka zurfafa hulɗa da masu zuba jari da faɗaɗa jerin ayyukan da ake shiryawa.

Game da zangon uku, ta ce an samu ƙarfafa haɗin gwiwa, bunƙasa ɓangarori, dawo da tsarin fasahar zamani da kuma tallafa wa jihohi. A ƙarƙashin OSIC, an karɓi tambayoyin masu zuba jari 672, an taimaka wa rijistar kasuwanci 189, adadi da ya zarce na zangon biyu. An kuma kammala sabunta SWIP.

A fannin PSI, ta ce an amince da buƙatu 14 a matakin farko, an tsawaita wasu 8, an bayar da takardun shaida 10, tare da samar da ayyuka kai-tsaye 2,416. Haka kuma, ana shirin sauya tsarin zuwa EDI nan da Janairun 2026.

Ta ce a fannin bayyananniyar bayanai, NIPC ta ƙulla haɗun gwiwa da Nairametrics domin rahoton zuba jari na lokaci-lokaci. A ɓangaren ƙasa da ƙasa, hukumar ta shirya dandalin zuba jari na Ogun–Brazil a taron BRICS na 17, ta shirya Brazil–Nijeriya tare da ApeɗBrasil wanda ya kai ga rattaba a yarjejeniyar fahimtar juna, tare da sauƙaƙa dandalin zuba jari na Delta–Brazil da Kaduna–Brazil. A taron TICAD 8 kuma, an sasanta yarjejeniya mai muhimmanci tsakanin Dangote da Mitsui.

Shugabar ta jaddada cewa burin NIPC shi ne juya sha’awar zuba jari zuwa ayyuka na gaske da ke samar da ayyukan yi da kuɗaɗen shiga, domin tallafa wa manufofin tattalin arzikin ƙasa.

A nasa jawabin, Shugaban ƙungiyar ‘Yan Jarida Masu Bibiyar Harkokin Kasuwanci da Masana’antu (CICAN), Ifeanyi Onuba, ya yaba da yadda NIPC ke ƙarfafa hazaƙar manema labarai, yana mai cewa kafofin watsa labarai na zama gada tsakanin manufofi da fahimtar jama’a, tare da alƙawarin ci gaba da rahoto mai inganci kan damar zuba jari a Nijeriya.

By ukarofi