Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Matatar Dangote ta sanar da fara sayar da man fetur a faɗin Nijeriya kan farashin Naira 739 a kan kowane lita, matakin da ake ganin zai kawo sauƙi ga jama’a tare da daidaita kasuwar man fetur a ƙasar.
A cewar sanarwar da kamfanin ya fitar, an fara aiwatar da sabon farashin ne a dukkan gidajen mai na kamfanin MRS, wanda ke da fiye da gidajen mai 2,000 a sassa daban-daban na ƙasar. Wannan na nufin cewa al’ummar Nijeriya za su fara cin gajiyar rage farashin a kusan dukkan yankuna.
Matatar ta yaba wa ’yan kasuwar da suka rungumi sabon tsarin farashi, tana mai kira ga sauran masu gidajen mai da su bi sahu domin tallafa wa farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa.
Kamfanin ya ce, nuna wannan kishin ƙasa zai taimaka matuƙa wajen rage raɗaɗin rayuwa da ’yan Nijeriya ke fuskanta.
A tarihi, lokutan bukukuwa kan kasance lokacin da ake fuskantar ƙarancin mai da hauhawar farashi.
Sai dai wannan mataki da Matatar Dangote ta ɗauka ya karya wannan al’ada, inda aka samu rage farashin man fetur a daidai lokacin da jama’a ke shirin bukukuwa. Matatar ta tabbatar da cewa tana da ikon samar da lita miliyan 50 na man fetur a kullum, lamarin da ke ƙarfafa tabbacin wadatar mai a kasuwa.
Masana na ganin cewa tace man fetur a cikin gida a wannan sikeli zai rage dogaro da kasuwannin waje, ya adana kuɗaɗen waje, ya arfafa darajar Naira tare da bunƙasa tsaron makamashi a Nijeriya. Rage farashin da kuma tabbacin wadatar mai na bai wa gidaje, ’yan kasuwa da masu sufuri numfashi a daidai lokacin da ake matuƙar buƙatar hakan.
Sai dai Matatar Dangote ta ja kunnen wasu ’yan kasuwa da ka iya yunƙurin ƙirƙirar ƙarancin mai domin hana jama’a cin gajiyar rage farashin. Ta buƙaci hukumomin gwamnati da su sa ido sosai tare da ɗaukar mataki mai tsauri kan duk wanda aka samu yana yunƙurin tada hankalin kasuwa, musamman a wannan lokaci mai muhimmanci.
