2026: Nijeriya za ta dakatar da shigo da ababen hawa marasa inganci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da sabon tsari mai muhimmanci a ɓangaren ƙira da shigo da ababen hawa, wanda zai fara aiki daga shekarar 2026, domin dakatar da shigo da motoci marasa inganci da ake kira ‘End-of-Life’ – wato motocin da suka riga suka daina amfani a ƙasashen da aka fito da su.

Matakin na da nufin kare masu amfani da mota, kare muhalli, bunƙasa tattalin arzikin sake sarrafa kayayyaki, tare da shirya ƙasar domin sauyin duniya zuwa motocin lantarki.

Darakta Janar na Hukumar Tsara da Ci gaban Motoci ta ƙasa (NADDC), Oluwemimo Joseph Osanipin, ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a karshen mako. 

Ya ce, kalmar End-of-Life na nufin motocin da ba su da izinin hawa hanya a ƙasashen da aka ƙera su ko aka yi amfani da su, amma wasu ‘yan kasuwa ke turo su Nijeriya domin cin riba.

A cewarsa, bincike ya nuna cewa wasu masu fitar da kaya daga ƙasashe kamar Japan na aika motocin da ba su da inganci zuwa Nijeriya, duk da cewa an riga an haramta musu amfani a ƙasashensu.

Ya ce sabon tsarin tantancewa da gwaji zai kawo ƙarshen wannan ɗabi’a, domin a ƙasashe masu ci gaba irin wazannan motoci ana mayar da su cibiyoyin sake sarrafawa, inda ake ciro sassan da za a iya amfani da su, sannan a zubar da sauran ta hanyar da ba ta cutar da muhalli.

Osanipin ya bayyana cewa a ƙarƙashin sabon tsarin, masu mallakar mota za su riƙa biyan wani kuɗi kaɗan a lokacin rajista, wanda za a yi amfani da shi wajen gina tsarin zubar da tsofaffin motoci, sake sarrafa su da kuma amfana da sassan da har yanzu suke da amfani a ƙarshen rayuwar mota.

Ya ce fiye da kashi 85 cikin 100 na sassan mota na iya sake amfani ko sarrafawa, lamarin da zai samar da ayyukan yi tare da bunƙasa kasuwar kayan gyaran mota na hannu-biyu.

Ya ƙara da cewa, idan aka tsara wannan tsarin yadda ya dace, tattalin arzikin sake sarrafa motoci zai iya samar wa Nijeriya sama da naira biliyan 150 a duk shekara, tare da rage matsalar motocin da aka yi watsi da su a kan tituna da kuma gurbatar muhalli.

Daga shekarar 2026, gwamnati za ta fara aiwatar da wajibcin tantance motocin da aka yi amfani da su kafin shigo da su Nijeriya.

A ƙarƙashin wannan tsari, za a riƙa gwada mota tare da ba ta takardar shaidar inganci tun daga ƙasar da aka fito da ita, kafin a turo ta Nijeriya. Masu shigo da mota ne za su dauki nauyin wannan gwaji, wanda aka kiyasta zai kai dalar Amurka 250 zuwa 300 a kowace mota. Duk wata mota da ta faɗi gwaji ko aka gano an yi mata maguɗi ba za a bar ta ta shiga ƙasar ba.

Haka kuma, Osanipin ya ce sabon tsarin ya tanadi alhakin mai ƙera kaya wato eɗtended producer responsibility, inda masu ƙera mota, masu tarawa da masu shigo da mota za su riƙa ɗaukar alhakin mota tun daga lokacin da aka ƙera ta har zuwa ƙarshen rayuwarta. Wannan tsari, inji shi, ya yi daidai da abin da ake yi a ƙasashe kamar Kanada, Japan da China.

Ya kuma bayyana cewa gwamnati na shirin Nijeriya domin sauyin duniya zuwa motocin lantarki. Ya ce Chana na shirin dakatar da rajistar motocin mai a cikin shekaru biyar masu zuwa, kuma hakan na iya janyo tura tsofaffin motoci zuwa wasu ƙasashe idan ba a yi hattara ba. Don haka, Nijeriya ta kara mayar da hankali kan horas da masu gyaran mota a fannin motocin lantarki da kuma canza motocin fetur zuwa iskar gas ta CNG.

A cewarsa, an riga an fitar da ƙa’idojin aikin yi na ƙasa (NOS) kan gyaran motocin CNG da na lantarki, kuma daga shekarar 2026 za a kara faɗaɗa su zuwa cikakkun littattafan horaswa da takardun shedar kwarewa a matakai daban-daban, domin tabbatar da cewa ‘yan Nijeriya sun zama kwararru masu gogayya a duniya.

Osanipin ya jaddada cewa waɗannan sauye-sauye ba wai dokoki kawai ba ne, illa kariya ce ga jama’a, muhalli da tattalin arzikin kasa.

Ya ce wayar da kan jama’a da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki zai zama ginshiƙin nasarar wannan tsari.

A ƙarshe ya ce, “Waɗannan manufofi na game da makomar Nijeriya ne – tabbatar da cewa jama’a na samun darajar abin da suka kashe, kare muhallinmu, da kuma sanya ƙasar a sahun gaba wajen sabuwar fasahar zirga-zirga ta zamani.”

By ukarofi