Manoman Jihar Nasarawa sun yaba da shirin FG/IFAD–VCDP

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafiya

Manoma a Jihar Nasarawa sun bayyana farin cikinsu da ci gaban da shirin Gwamnatin Tarayya tare da IFAD na Value Chain Development Programme (VCDP) ke kawowa, inda suka ce shirin ya sauya fasalin harkokin noma tare da ba su fata na samun girbi mai yawa da riba.

Manoman sun ce matakin da gwamnatin Jihar Nasarawa ta ɗauka na ci gaba da aiwatar da shirin VCDP har bayan shekarar 2026 ya ƙara musu kwarin gwiwa, musamman ganin yadda shirin ke tallafa musu da horo, kayan aiki da dabarun zamani na noma.

Sun bayyana hakan ne a yayin wani taron kwana guda na masu ruwa da tsaki a harkokin noma da aka gudanar a Lafiya, fadar gwamnatin jihar, domin tattauna hanyoyin karfafa aiwatar da shirin VCDP da kuma ɗorewar sa a jihar.

Da yake jawabi a wajen taron, Kwamishinan Noma na Jihar Nasarawa, Honorabul Tanko Tunga, ya ce gwamnatin jihar ta ƙuduri aniyar tabbatar da ci gaba da aiwatar da shirin VCDP saboda irin gagarumar gudunmawar da yake bayarwa ga bunƙasar noma da rayuwar manoma.

Ya ce, gwamnatin ta fahimci muhimmancin shirin, musamman wajen ƙara yawan amfanin gona, haɓaka kuɗin shiga da kuma bunƙasa tattalin arzikin jihar. A cewarsa, duk da yiwuwar fuskantar wasu ƙalubale a lokacin aiwatarwa, gwamnatin ba za ta ja da baya ba.

A nata ɓangaren, Kodinetar shirin VCDP a jihar, Dakta Eunice Adgidzi, ta bayyana cewa ci gaba da shirin zai kara wa manoma ƙwarewa, inganta dabarun noma da kuma samar da wadatattun girbi masu amfani, wanda hakan zai amfanar da jihar Nasarawa da ƙasa baki ɗaya.

Ta ce shirin na VCDP ya zamo ginshiƙi wajen tallafa wa manoma, musamman masu noman shinkafa da rogo, ta hanyar horo da tallafin kayan aiki na zamani.

Shi ma dan Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa mai wakiltar mazaɓar Obi I, Dakta Peter Akwe, wanda shi ne shugaban kwamitin harkokin noma na majalisar, ya ce shirin VCDP ya nuna tasiri sosai ga manoman jihar.

Ya yi alƙawarin cewa majalisar dokoki za ta ci gaba da bayar da goyon bayan doka da tsare-tsare domin tabbatar da dorewar shirin a faɗin jihar.

A ƙarshe, Jami’in kula da Ilimi da Sadarwa na shirin VCDP a jihar, Samson Jonath, ya bayyana cewa zuwa yanzu shirin ya horar da manoma 62 kan hanyoyin sarrafa takin zamani da dabarun noman shinkafa da rogo.

Haka kuma, ya ce manoma 393 sun amfana da tallafin iri na shinkafa da rogo a kananan hukumomi biyar na jihar, wanda ya taimaka wajen ƙara yawan amfanin gona da ingancin girbi.

By ukarofi