Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mawaƙin Amurka Darryl Dwayne Granberry Jr. da aka fi sani da DDG, ya bayyana farfagandar kafafen watsa labaran ƙasashen yammacin duniya akan Nijeriya a matsayin “bogi”.
Tauraron na ‘Hip-hop’, wanda a yanzu yake hutu a Legas, ya ce saɓanin farfagandar ‘yan Yamma, Nijeriya ba ta yi kusa da Amurka ba wajen zama haɗari ga al’umma.
DDG ya kuma roƙi ‘yan ƙasashen waje da su ziyarci Nijeriya domin gane wa idanunsu ko akwai gaskiya akan abin da ake yaɗawa game da Nijeriya.
Da yake jawabi yayin wata hirar bidiyo, mawaƙin Amurkan ya ce: ” A ƙashin gaskiya Ina ganin Amurka ita ce ƙasa mafi haɗari. Ba na tunanin Nijeriya tana da haɗari kamar Amurka – A’a ko kusa.”
Ya ƙara da cewa, babu shakka cewa akwai rashin tsaro a Nijeriya, “amma tarzomar bindiga da dabanci ba ababen da suka shahara a Nijeriya kamar Amurka ba ne. Don haka, idan wani yana son zuwa Nijeriya, ya yi azama.”
Kazalika, ya bayyana cewa an sanar da shi cewa kalolin abinci Nijeriya ba su da nagarta ga lafiya, zancen da ya ƙaryata da cewa suna da kyau ga lafiya sosai “musamman dafa-duka”.
