Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani sabon rikici ya kunno kai yayin da Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na Jihar Bauchi a ranar Alhamis ya zargi Ministan Abuja, Nyesom Wike da yunƙurin ɓata masa suna da lalata mutuncinsa a idon jama’a a siyasance.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin a wata hira da da gidan talabijin na Channels, inda ya ce ana jifan sa da wasu zarge-zarge marasa tushe ciki har da alakanta shi da batun ta’addanci da ‘yan bindiga, lamarin da ya musanta.
A cewarsa, Jihar Bauchi na daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Arewa maso Gabas, kuma hakan ya samu ne ta hanyar hikima da dabaru ba tare da wata alaka da laifuka ba.
Ya ce ana yi masa haka ne saboda yana daga cikin manyan ‘yan adawa, inda ya kuma zargi Wiken da taɓa yin barazanar cinna wuta a Jihar Bauchi, wanda a yanzu kuma yake aiki da barazanar wajen ɗaukar nauyin rikicin siyasa da neman a yi bincike akan gwamnatinsa.
Gwamna na Bauchi ya kuma ce zai kare kansa a dukkan matakai, yana mai cewa ya riga ya aike wa Antoni Janar na Ƙasa tare da sanar da hukumomin tsaro, kuma zai kai ƙorafinsa ga ƙasashen duniya saboda abin da ya kira da “tauye masa ‘yancin ɗan-adam” da dokar ƙasa ta ba shi.
Ya ƙara da cewa, ana amfani da EFCC wajen muzguna masa da wasu jami’an gwamnatinsa saboda ƙin amince wa Bukar komawa jam’iyyar APC.
A ƙarshe, ya musanta zargin sa da hannu a ayyukan ‘yan bindiga, yana mai cewa jiharsa tana zaune ƙalau ne sakamakon dabaru, leƙen asiri da kuma shugabancin surkawa da al’umma.
