Adamawa: Shugaban ƙaramar hukuma ya nemi a tura sojoji bayan Boko Haram sun halaka mutane 14

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Aƙalla mutane 14 ne aka halaka a wani mummunan harin da mayaƙan Boko Haram suka kai wa wasu ƙauyuka biyu a Ƙaramar Hukumar Hong da ke Jihar Adamawa, lamarin da ya janyo sabunta kiraye-kirayen ƙarfafa dakarun sojoji a yankin.

Shugaban ƙaramar hukumar, Usman Inuwa ya tabbatar da faruwar al’amarin a yau Junairun, yana mai cewa maharan sun kai farmaki ne a ƙauyukan Mubang da Zar a ɗaya daga cikin dararen makon da ya gabata.

A wata hira da manema labarai ta salula, Inuwa ya ce da misalin ƙarfe 9 na dare mayaƙan suka kai farmakin inda a nan ne suka halaka mutane sha huɗun da raunata wasu biyu gami da banka wa gidaje da dama wuta da wuraren abinci.

A cewarsa, ƙauyukan, waɗanda suna wani yanki ne da ke kusa da Dajin Sambisa, wato maɓoyar mayaƙan, na kewaye da babban wuri da ba mutane, wanda ke ba su damar kai hare-hare cikin sauƙi.

Shugaban ya kuma tsaron yankin ya dogara ne da sintirin haɗaka na sojoji da ƴan bijilante, waɗanda sun sha daƙile harin mayaƙan.

Ya ƙara da cewa, a watan Disamba ‘yan Boko Haram sun yi yunƙurin kai hare-hare har sau uku a ƙauyukan, saidai ba su yi nasara ba saboda mayar da martani daga ɓangaren jami’an.

A ƙarshe, ya bayyana cewa, kusanci ƙauyukan da dajin na Sambisa ya zama babban ƙalubalen tsaro, yana mai kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta tura ƙarin jami’an sojoji tare da ƙaddamar da farmaki ta sama akan guraben mayaƙan da ke yankin.

By ukarofi