Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ƙungiyar shugabannin hukumomi da ma’aikatun gwamnatin Jihar Kano sun buƙaci jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, da ya jagorance su tare da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.
Shugaban ƙungiyar Alhaji Tukur Wada Sagagi ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a ranar Lahadi a Kano.
Buƙatar hakan ta fito ne bayan wani taro da shugabannin hukumomin suka gudanar, inda suka ce sun yi la’akari da halin da siyasa jihar ke ciki a halin yanzu, inda suka ce komawa APC shi ne abun da zai taimaki jihar Kano.
Ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen kare makomar siyasar Kano tare da tabbatar da haɗin kai a tsakanin shugabannin jihar.
Taron ya samu halartar kusan shugabannin hukumomi 70, na hukumomin da ma’aikatun gwamanatin Jihar Kano.
“Muna roƙon jagoranmu, Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, da ya jagorance mu tare da gwamnanmu, Alhaji Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC. Mun yi imanin cewa wannan ne mafi dacewa ga cigaban jiharmu.” Inji Alhaji Tukur Sagagi
Kazalika, kungiyar ta kuma bayyana cewa a shirye take tsaf domin shiga jam’iyyar APC, tare da alƙawarin haɗa kai wajen ƙarfafa jam’iyyar da kuma inganta zaman lafiya da ci gaba a Jihar Kano.
Daga bisani shugabannin ƙungiyar sun kuma je ofishin sabon shugaban jam’iyyar NNPP na Jihar Kano Alhaji Abdullahi Zubairu Abiya domin yi masa mubaya’a tare da ba shi tabbacin za su ba shi duk wata gudanarwa don ya sami nasarar da ake fata.
Sun kuma sha alwashin cigaban da marawa gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf baya domin cigaba da yin aiyukan alheri.
