Ina son in ga mata suna taimaka wa junansu – Aisha Lawal Umar 

Spread the love

“Mutane suna yi wa mata ýan jarida mummunar fahimta”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU 

(Ci gaba daga makon jiya)

Mai karatu barkanmu da sake ganin zagayowar sati lafiya. Idan ba ku manta ba, a makon da ya wuce mun kawo maku tattaunawa da muka fara da shahararriyar ‘yar jarida kuma jajirtacciya akan aikinta, ɗaya daga cikin matan da ke gabatar da shirin Zamantakewa na gidan talabijin na Arewa24, Aisha Lawal Umar wadda ta soma da bayyana mana tarihinta zuwa bayani kan asalin yadda aka ƙyanƙyashe shirin na Mata A Yau. 

Kamar yadda muka yi alƙawarin kawo karashin tattaunawar tamu, za mu soma da amsa tambayar da muka yi sallama kanta, kafin wasu tambayoyin. A sha karatu lafiya. 

MANHAJA: Wanne ƙalubale ki ka fi fuskanta a yanayin aikin da ki ke yi?

AISHA LAWAL: Babban ƙalubalen da nake fuskanta bai wuce yadda duk abin da ka yi ba ka iya burge mutane ba. Kuma duk yadda ka yi mutane ba za su fuskance ka ba, sai a hankali wasu ke gane ina aka dosa. Kawai ni abin da ya fi ci min tuwo a ƙwarya shi ne yadda mutane suke yi mana mummunar fahimta, duk da kasancewar an san mu, wasu har iyayenmu sun sani. An san mu Hausawa ne, mu musulmi ne, ba yadda za a yi mu daɓawa kanmu wuƙa ko mu cutar da addininmu ko al’adarmu, mu ma ƙoƙari muke yi mu ba da gudunmawa don a gyara, amma sai ka ga wasu na ta yaɗa farfaganda a kanmu, da zarge-zarge marasa ma’ana. Amma Allah Ya sani. Ni dai ban taɓa ganin wani abu ya zo teburina a ce wai dole in yi shi ba. Ni nake tsara duk wani shiri da Arewa24 take gabatarwa, a ƙarƙashin ofishina, ba yadda za a kawo min wani ra’ayi da bai dace da addinina da al’adata ba kuma in yi shi. Duk abin da muka gabatar sai da muka yi bincike muka tabbatar da ingancinsa kafin muka shirya shirin akai. Ba na jin daɗin aibata mu da ake yi, kodayake ba na sa shi a raina ya hana ni yin abin da nake yi, saboda na san ban kaucewa koyarwar addinina da al’adata ba.

Idan za a baki zaɓi ki canza wani abu a rayuwarki, wanne abu za ki so ki canza, saboda yadda ki ka kalli abin a baya?

Wallahi babu. Ina jin daɗin yadda nake gudanar da rayuwata a halin yanzu. Wataƙila da zan canza wani abu ba zai wuce yarda da dogaro ga Allah ba. Da tuni na fahimci Allah ne ke bayarwa, kuma shi ne ke yin komai, da ban bai wa kaina wahala kan wasu abubuwan ba.

Wanne buri ki ke da shi a rayuwarki?

Ina son in ga na yi wa mahaifiyata hidima sosai, in ga ina faranta mata rai tana jin daɗi. Ina son mamana sosai gaskiya. Amma Alhamdulillah. Ina da burin na ga kowacce mace ta tsaya da ƙafafunta. Ina son in ga mata suna taimakawa junansu mata. Babban burina in ga zan iya taimakawa duk wanda yake neman taimako a wajena. Ina kuma da burin in ga na gama da duniya lafiya.

Idan ba kya wajen aiki ko wata hidima ta iyali, me ki ka fi yi wanda yake sa ki nishaɗi?

To, ni ba mutum ce mai son yawo ba. In dai ba na gida to, ina wajen aiki. In ka ga na je waje to, ya zama dole ne in je. Na fi so in zauna a gida da yara, in kalli fim in basa nan. Na ma fi jin daɗi in ba sa nan, don ban son hayaniya, ko wani waje na je idan ana hayaniya, sai in ji na takura sosai. Kuma bani da ƙawaye da yawa. Na kan ɗan yi tafiya lokaci zuwa lokaci, bayan wata uku zuwa huɗu haka. Ba ni da son yawo gaskiya. 

Wanne tasiri shirinki na Zamantakewa yake yi a rayuwar ma’aurata?

Wato, shi shirin Zamantakewa daɗaɗɗen shiri ne da nake gabatarwa don tattauna matsalolin iyali, ba akan mata ba ne kawai, har da maza ma. Duk wanda muka lura ana samun yawan ƙorafi kan abubuwan da yake yi, muna zama tare da baƙin da muke gayyatowa don a tattauna akai. Kuma yana samun karɓuwa sosai har a gun maza, don wani lokaci su da kansu suke kira suna bayyana yadda suke jin daɗin shirin da kuma tasirin da yake yi a kansu. Akwai wani da ya taɓa yin takakkiya tun daga Abuja, don har ofishin mu domin ya bayyana mana yadda shirin ya yi tasiri a rayuwarsa da ta iyalinsa. Don haka zan ce lallai shirin Zamantakewa yana tasiri sosai.

Da me ki ke so a riƙa tunawa da ke bayan ba kya raye?

Ko yanzu Alhamdulillah. Nasan duk wani wanda ya zo Arewa24 a matsayin mai gabatarwa, ba fariya ba, in ma ba ni na ɗauke shi ba to, ina da hannu a ɗaukarsa aiki. Ko kuma ni na koya masa yadda ake gabatar da shirye-shirye. Alhamdulillah,  na koyar da ma’aikata da daman gaske, wasu a Arewa24, wasu kuma a wasu wurare. Ina son ko na mutu wani ya tuna da ni ya ce, wance ce ta koya min aiki ko wance ce sanadin na samu aiki da sauran su. Ina son in ga na taimaka wa mutane,  a kowanne yanayi, don in ga rayuwar sa ta yi kyau ko ta inganta. Ina son ko ba na nan wani ya tuna cewa na taimake shi, a sha’anin aiki ko a rayuwarsa. Na san wasu za su ga kamar ina takura musu ko wani abu mai kama da haka, amma na yi imanin wata rana wani zai tuna bayan ya ga tasirin abin da na yi masa. Na gode wa Allah da irin rayuwar da nake yi, kuma ban taɓa yin nadama kan wani abu da na yi ba. Duk abin da ya same ni na yi  imanin daga Allah ne, kuma duk abin da Allah Ya ƙaddara min na yi imanin akwai hikima da alheri a cikinsa.

Wanne irin launi ne ya fi baki sha’awa, na sutura ko na wani abu da ki ka fi mu’amala da shi?

Launin tsanwa, mai ruwan ƙasa!

Idan kin samu dama wacce ƙasa ki ke sha’awar zuwa don hutawa ko yawon buɗe ido?

ƙasar Oman.

Idan za a baki mulkin ƙasar nan na wuni guda, wanne abu za ki so ki ga kin gyara?

Babban abin da ya fi damuwa a ƙasar nan ba rashin ilimi ba ne ko rashin ƙwararru. Yawan rashin gaskiya da cin amana, a kowanne fanni na rayuwa shi ne ya fi damuna. Ba ga mazan ba, ba ga matan ba. Domin hatta matan ma idan aka ba su amana a sha’anin gwamnati, muna ganin yadda suke almundahana da warwason dukiyar talakawa. Gaskiya wannan zaluncin da rashin gaskiyar shi ne ya fi ci min tuwo a ƙwarya. Don haka, abin da zan fara gyarawa idan na samu dama shi ne zan tabbatar duk wanda za a bai wa wani muƙami ko damar riƙon wani nauyi to, ya zama cancantarsa ce ta sa aka ba shi, ba hidimar da ya yi a siyasa ba, ko don wani ubangida da yake da shi.

Wacce karin magana ce take tasiri a rayuwarki?

Akwai dai wata magana da nake ji ana faɗa,  ban sani ba ko karin magana ce ko wa’azi ba ne, amma yana tasiri a rayuwata. Ana cewa, kowa ya dogara ga Allah to, Allah ya isar masa!

Na gode.

Alhamdulillah,  ni ma na gode.

By ukarofi