Motocin Ambulance da gwamna Dikko Raɗɗa ya yi oda sun iso Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Da yake magana da manema labarai a Katsina shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Hon Abdukadir Andaje ya ce waɗannan motoci ɗaukan marasa lafiya za a ajiye sune a muhimman wurare a manyan hanyoyin jihar.

Ya ce ganin yadda gwamnatin Dikko Raɗɗa ta giggina manyan hanyoyi tare da gyara wasu da suka lalace akwai yiwuwar masu ababen hawa su ƙara gudu a manyan hanyoyin ba tare da la’akari da lafiyar ababen hawar su ba.

Andaje ya bayyana cewa ganin irin tuƙin ganganci da ka iya faruwa yasa gwamna Dikko Raɗɗa ya yi odar waɗannan motoci domin zirga-zirga a manyan hanyoyin jihar.

Ya ce dama can a lokacin da yake yaƙin neman zaɓe, gwamna Raɗɗa yayi alƙawarin samar da irin waɗannan motoci domin ɗaukar mara lafiya ko waɗanda suka sami haɗari cikin gaggawa zuwa asibiti.

Shugaban ma’aikatan ya sanar da cewa, gwamnati za ta kafa kwamiti da zai rinƙa lura da kaiwa da komowa da kuma lafiyar motocin.

Acewar sa kwamitin zai ƙunshi jami’an hukumar kiyaye haɗurra na ƙasa, ‘yan sandan da ma’aikatan lafiya.

Abdulkadir Andaje ya yi bayani dalla dalla kan wasu aikace-aikacen da gwamnatin Dikko Raɗɗa ta gudanar kan kiwon lafiya.

Motocin ƙirar Toyota sun ƙunshi kayan agajin gaggawa ga marasa lafiya kafin a kai shi asibiti.

By ukarofi