Yanzu-yanzu: Bom ya yi ajalin sojoji tara a hanyar Maiduguri zuwa Gubio

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Kimanin sojoji guda tara ne suka rasa rayukansu a sakamakon fashewar wasu boma-bomai akan babban titin Maiduguri zuwa Gubio a Jihar Borno, lamarin da majiyoyin tsaro suka bayyana a matsayin farmakin da mayaƙan Boko Haram suka kitsa.

Rahotanni sun bayyana cewa, al’amarin ya faru ne a daren Lahadi wayewar Litinin akan hanyar, wadda sojoji da fararen hula ke yawan zirga-zirga ta ita a arewacin Borno.

An gano cewa dakarun da iftila’in ya afka wa sun tafiya ne daga Maiduguri zuwa Gubio domin gudanar da wani atisaye a Dajin Sassawa da ke kusa da Jihar Yobe.

Da suke tabbatar wa manema labarai al’amarin a Maiduguri majiyoyin tsaro da na CJTF sun ce binciken farko ya nuna cewa mayaƙan sun dasa boma-boman ne da tsakar dare da nufin tarko ga dakarun.

A cewarsu, sojojin waɗanda aka tura ne daga Bataliya ta 145 da ke Damasak a ƙarƙashin Birget na 5 na Rundunar Sojin Nijeriya na Barikin Maimalari, Maiduguri.

Haka kuma, an ruwaito cewa sojojin sun bar Maiduguri tun a ranar Asabar, inda suka ya da zango a wani shingen sojoji da ke gefen titi a kusa da garin Gubio da nufin cigaba da tafiyar a washe gari.

Al’amarin ya faru ne a lokacin da suka cigaba da tafiya a ranar Lahadin inda aka samu tashe-tashen boma-bomai. Bayan waɗanda suka rasu, akwai kuma waɗanda suka jikkata, lamarin da ya sa aka garzaya da su asibiti.

By ukarofi