Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
Masarautar Ringim ta yi gargaɗi ga masu unguwanni, dagatai da hakimai da su guji yin duk wani abu da zai zama zagon ƙasa ga ayyukan Hukumar Hisba, tare da umartar su da su bai wa hukumar cikakken haɗin kai domin ta gudanar da aikinta yadda ya kamata.
Mai Martaba Sarkin Ringim, Alhaji Sayyadi Mahmood, ya bayyana cewa duk wanda aka samu daga cikin dagatai, masu unguwanni ko hakimai yana yi wa Hukumar Hisba yankan baya, masarautar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakin tsige shi, ko wanene shi.
Masarautar ta Ringim ta kuma tabbatar wa Hukumar Hisba da cikakken goyon bayanta wajen gudanar da ayyukanta. Wannan jawabi ya fito ne daga bakin Ciroman Ringim, Alhaji Aji Usman Sayyadi, wanda ya wakilci Mai Martaba Sarkin Ringim a yayin da ya karɓi bakuncin Shugaban Hukumar Hisba ta ƙaramar hukumar Ringim, Alhaji Fa’iz Muhammad Bashir, a fadar masarauta.
Mai Martaba ya bayyana cewa aikin Hisba aiki ne na Allah, kuma masarautar a shirye take ta mara wa hukumar baya domin taimakawa wajen hana yaɗuwar baɗala da munanan ayyuka a cikin al’umma. Ya ƙara da cewa tun da aikin Hisba shi ne kare Musulunci, masarautar Ringim ma tana daga cikin masu kare addinin Allah da martabar Musulmi.
Sarkin ya shawarci jami’an Hukumar Hisba da su ji tsoron Allah wajen gudanar da ayyukansu, tare da bin dokoki da ƙa’idojin da aka kafa hukumar a kai. Haka kuma ya buƙace su da su ƙara maida hankali waje n gyaran tarbiyyar matasa, da hana su shiga harkokin shaye-shaye, amfani da miyagun ƙwayoyi da aikata sauran munanan ayyuka.
Mai Martaba ya nuna matuƙar damuwarsa kan yadda matsalar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi ke barazana ga rayuwar matasa, yana mai kira ga Hukumar Hisba da ta haɗa kai da masarautar Ringim domin daƙile wannan matsala, musamman ta hanyar hana shan miyagun ƙwayoyi da aikata baɗala a cikin al’umma.
