
Rundunonin jami’an tsaro sun tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen harabar Gidan Gwamnatin Jihar Kano a jiya Litinin, sakamakon rahotannin da ke yawo kan yiwuwar sauya sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa Jam’iyyar APC.
Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaron sun hallara domin tabbatar da zaman lafiya da kuma hana duk wani abu da ka iya tayar da hankalin jama’a.
An ruwaito cewa jami’an tsaron da aka jibge sun haɗa da ’Yan Sanda da kuma jami’an tsaron farin kaya DSS, inda aka kafa su a babbar ƙofar shiga gidan gwamnatin da sauran muhimman wurare.
Haka kuma, an ga aƙalla motoci masu sulke guda bakwai na jami’an tsaro, tare da ƙara tsaurara bincike ga duk wanda ke shiga harabar gidan gwamnatin.
Duk da cewa ba a fitar da wata sanarwa a hukumance kan shirin ficewar gwamnan ba, amma ana raɗe-raɗin cewa yana shirin komawa Jam’iyyar APC.
Hakan ya sa hukumomin tsaro suka ɗauki matakan kariya domin kauce wa duk wani rikici, tare da tabbatar da cewa zaman lafiya da doka da oda sun cigaba da wanzuwa a jihar.
