Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau
Wani mazaunin Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara, Sanusi Lalan Gusau, yayi Kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya sallami ƙaramin ministan Tsaro Hon Bello Mohammed Matawalle daga muƙamin sa.
Yayi wannan kiran ne a hirarsa da manema labarai yau Litinin a Gusau.
A cewar sa, ƙaramin ministan tsaron ya gaza a ɓangaren kawo karshe ta’addanci da ya addabi al’ummar Jihar ta Zamfara tun lakacin da ya zama ministan.
Sanusi Lalan ya bayyana cewar kiran ya zama wajibi la’akari da halin ƙuncin rayuwa da alummar jihar Zamfara su ka samu kansu, sakamakon ayyukan ta’addanci.
Yana mai jaddada cewar tuni ya rubuta takardar ƙorafin ga ofishin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Ya bayyana cewar, siyasantar da lamarin tsaro ya jefa Jihar cikin mummunan yanayin tashin hankali, yana mai nuni da cewar ba zai yi ƙasa a gwiwa ba har sai buƙatar shi ta biya.
“Bazanyi ƙasa a gwiwa ba har sai buƙatar da na sanya a gaba ta biya, Kuma ban damu da kowanene za a baiwa ministan tsaron ba in har an cire Matawalle “. Ya ƙara da cewa
